Duk da barazanar amfani da bindiga: Yan Shi'a sun gunar da zanga zanga a Abuja

Duk da barazanar amfani da bindiga: Yan Shi'a sun gunar da zanga zanga a Abuja

- Mabiya akidar Shi'a sun gudanar da zanga zanga a babban birnin tarayya Abuja

- Sun shirya gudanar da zanga zanga a ranar Alhamis don tunawa da ranar Ashura

- Tawagar masu zanga zangar na bayyana bukatar gwamnatin tarayya ta saki shugaban su, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky

Ayyukan yau da kullum a babban birnin tarayya Abuja ya tsaya cak! biyo bayan wata zanga zanga da mabiya akidar shi'a IMN suke kan gudanarwa, bayan da suka bijirewa barazanar da jami'an tsaro na yan sanda suka yi masu na amfani da bindiga ma damar suka ce za su gudanar da zanga zangar.

Sun fara zanga zangar ne daga titin Aguyi Ironsi, Maitama, sakamakon rufe dukkanin hanyoyi da jami'an soji suka yi da zai kai su ga babbar sakatariyar gwamnatin tarayya, don dakile su daga shiga cikin ginin.

Mabiya akidar Shi'ar, sun shirya gudanar da zanga zanga a ranar Alhamis don "bukin bakin cikin ranar da aka kashe Sayyadina Hussaini," a cewar su, bikin bakin cikin da suke gudanarwa a kowace shekara, mai taken 'tunawa da ranar Ashura'.

Duk da barazanar amfani da bindiga: Yan Shi'a sun gunar da zanga zanga a Abuja
Duk da barazanar amfani da bindiga: Yan Shi'a sun gunar da zanga zanga a Abuja
Asali: Original

Sai dai hankula sun fara tashi ne a lokacin da rundunar yan sanda ta mamaye manyan yankuna uku na birnin tarayyar, inda suka dakatar da zirga zirgar ababen hawa da mutane. Wannan ya sa masu zanga zangar suka nuna tilas akan barinsu ci gaba da zanga zangar har zuwa sakatariyar gwamnatin tarayya don cika bikin bakin cikin wannan rana.

KARANTA WANNAN: Wani makaho da mutane 3 sun gamu da ajalinsu a ambaliyar ruwan Delta

Masu zanga zangar sun ce a shirye suke su tari duk wata barazana da ke tunkaro su, inda har aka ga wasu suna tara duwatsu a bakin tituna don jiran ko ta kwana daga rundunar yan sanda.

Daga bisani masu zanga zangar suka kutsa ta cikin turakun hana wucewa don samawa kansu hanyar wucewa don zuwa sakatariyar gwamnatin tarayyar, inda suka yi kunnen uwar shegu da umarnin yan sandan da ke rike da bindigogi a cikin shirin jiran umarni.

Sun ci gaba da zanga zangar har zuwa hanyar Shehu Shagari, inda suke kiran "A saki Sheikh Zakzaky"

Tawagar masu zanga zangar na bayyana bukatar gwamnatin tarayya ta saki shugaban su, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky, wanda ya ke tsare a hannun jami'an tsaro tun a ranar da aka yi wani karon batta tsakanin yan shi'ar da tawagar hafsan hafsosin sojan sama, Tukur Buratai a Zaria, shekara ta 2015.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel