Boka da wasu mutane biyu sun cizge idanuwan dan sanda domin tsubbu, an damke a jihar Katsina

Boka da wasu mutane biyu sun cizge idanuwan dan sanda domin tsubbu, an damke a jihar Katsina

Wani boka da shekara 80 mai suna Usaini Musa da wasu mutane biyu sun shiga hannun jami’an yan sandan jihar Katsina sanadiyar laifin cizge idanuwa wani jai’in yan sanda a jihar Flato

Kwamishanan yan sandan jihar Katsina, Muhammadu Wakili, a wani hira da manema labarai ya bayanna sunayen wandannan mutane Abubakar Sani, 35 da Abubakar Muhammed, 28.

Jaridar Punch ta samu labarin cewa Sani mazauni Katsina ne, Muhammad da Musa kuma mazauna garin Jos.

Kwamishanan ya kara da cewa dan sandan da suka cirewa ido, Sajen Umana Ishaya, yana aiki karkashin rundunar Operation Safe Haven, a Jos lokacin sannan suka kashe shi.

Abubakar Sani da Abubakar Muhammadu sun bukaci bokan ya basu layar bata da zai taimaka musu wajen shiga gidajen mutane su saci kudi ba tare da an gansu ba.

KU KARANTA: Tinubu, APC, na kokari tursasa Ambode janyewa daga takarar gwamnan jihar Legas

Bokan ya umurcesu da cewa su nemo idanuwan wani mutum domin hada tsubbun za suyi amfani da shi.

Kwamshanan yace: “Yan barandan sun amince da zargin da ake musu, kowannensu ya bayyana rawan da ya taka. Za’a gurfanar da su muddin an kammala bincike.”

Daga cikin abubuwan da aka gano daga hannunsu har da idon jami’a dan sandan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel