Ambaliyar ruwa ta cinye wata karamar hukuma a jihar Jigawa

Ambaliyar ruwa ta cinye wata karamar hukuma a jihar Jigawa

- Ambaliyar ruwa ta yi sanadin hijirar mutanen karamar hukumar Auyo da ke jihar Jigawa, bayan da ambaliyar ta cinye cikin garin gaba daya

- Sama da mutane 300 ne suke kan kwale kwale don ficewa daga garin

- An samu asarar ran mutum daya, inda gidaje da gonaki suka dulmiye a cikin ambaliyar

Rahotannin da Legit.ng ta samu ya tabbatar da cewa ambaliyar ruwa ta yi sanadin hijirar mutanen karamar hukumar Auyo da ke jihar Jigawa, bayan da ambaliyar ta cinye cikin garin gaba daya.

Mai magana da yawun shugaban karamar hukumar Auyo, Alhaji Abdullahi Olu, ya bayyana cewa sama da mutane 300 ne suke kan kwale kwale don ficewa daga garin yayin da tuni sauran jama'ar garin suka yi hijira don tsira da rayukansu daga wannan mummunar ambaliyar.

Wadanda suka samu damar yin hijirar, sun nausa wasu kananan hukumomi na jihar ta Jigawa don neman mafaka, kamar su kananan hukumomin Kafin Hausa, Kaugama, Hadejia, Malam Madori da dai sauransu, yayin da wasu suka ketara zuwa karamar hukumar Ningi da ke jihar Bauchi.

KARANTA WANNAN: Mutane 10 sun mutu a harin da wasu yan ta'adda suka kai ana tsakiyar taron APC a Abia

Ambaliyar ruwa ta cinye wata karamar hukuma a jihar Jigawa
Ambaliyar ruwa ta cinye wata karamar hukuma a jihar Jigawa
Asali: Twitter

Ko da aka tambayi Alhaji Abdullahi Olu Auyo, dangane da asarar rayuka ko dukiya, ya ce: "Zuwa yanzu babu wani tabbaci na adadin mutanen da suka rasa rayukansu, ama muna da masaniyar mutuwar mutum daya.

"Dangane da asarar dukiya kuwa, wannan babu kiyascin kudi, domin kusan gaba daya gidajen garin sun rushe, wasu sun nutse, kaga kuwa duk wata dukiya da ke cikin gidajen sunbi ruwa. Haka zalika amfanin gonar dubunnan mutane sun salwanta a ruwan," a cewar Abdullahi Auyo.

Da ya ke jinjinawa gwamnatin jihar Jigawa bisa namijin kokarinta na kai masu dauki, mai magana da yawun shugaban karamar hukumar Auyo, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka ta kawo masu agajin gaggawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel