Mutane 10 sun mutu a harin da wasu yan ta'adda suka kai ana tsakiyar taron APC a Abia

Mutane 10 sun mutu a harin da wasu yan ta'adda suka kai ana tsakiyar taron APC a Abia

- Sama da mambobin jam'iyyar APC 10 ne ake sa ran sun mutu a jihar Abia, sakamakon harin da wasu yan ta'adda suka kai

- Wani mamban jam'iyyar da ya bayyana sunansa da Obioma Achonna ya ce yan ta'addan sun kwace masa N30,000

- Kwamishinan yan sanda na jihar Abia, Mr. Anthony Ogbizi, ya ce ba shi da masaniya akan wannan harin

Sama da mambobin jam'iyyar APC 10 ne ake sa ran sun mutu a jihar Abia, sakamakon harin da wasu yan ta'adda suka kai a lokacin da 'yayan jam'iyyar ke gudanar da taro a kauyen Okpuala Aro, karamar hukumar Osisioma Ngwa.

Majiya ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta shaidawa kamfanin jarida na Vanguard cewa 'yayan jam'iyyar APC na garin sun gana da wata yar takarar sanata a mazabar Abia ta tsakiya, Sanata Nkechi Nwaogu, wacce ta zo yakin neman zabe a kauyen.

Jim kadan bayan tafiyar ta tare da tawagarta, mambobin jam'iyyar sun kuma taru don tattauna wasu batutuwan. Yan ta'addan suka riske su wajen taron, inda kai tsaye suka fara dukan shugaban jam'iyyar na gundumar Osisio,a Ngwa ta 4, Mr. Chibuike Nwaohanmuo.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Shugaban kasa Buhari ya dakatar da Sifetan yan sanda daga binciken takardun Sanata Adeleke

A cewar majiyar, shugaban jam'iyyar ya suma sakamakon wannan dukan, inda daga baya ne aka garzaya da shi wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba. Da yawa daga cikin mambobin jam'iyyar sun samu raunuka yayin da wasu suka gudu don neman mafaka, bayan da yan ta'addan suka zaro makamai.

Mutane 10 sun mutu a harin da wasu yan ta'adda suka kai ana tsakiyar taron APC a Abia
Mutane 10 sun mutu a harin da wasu yan ta'adda suka kai ana tsakiyar taron APC a Abia
Asali: Twitter

Wani mamban jam'iyyar da ya bayyana sunansa da Obioma Achonna ya ce yan ta'addan sun kwace masa N30,000 tare da yi masa dukan kawo wuka. Haka shima wani mamban jam'iyyar, Ihechi Nwankwo ya ce an sare shi a saman kansa da adda a lokacin da ya ke kokarin tserewa daga wajen.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu tawagar soji da ke a wani gari kusa da inda lamarin ya afku sun ki kai dauki, sai babu wani tabbas na gaskiyar wannan rahoto har zuwa lokacin da aka rubuta wannan labari.

Kwamishinan yan sanda na jihar Abia, Mr. Anthony Ogbizi, ya ce ba shi da masaniya akan wannan harin, haka shima kwamandan rundunar da ke yankin da lamarin ya faru, bai tabbatar da faruwar harin ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel