Zan gyara Najeriya cikin shekaru 2 kacal - Wani dan takarar shugaban kasa

Zan gyara Najeriya cikin shekaru 2 kacal - Wani dan takarar shugaban kasa

- David Mark yace zan gyara Najeriya cikin shekaru 2 kacal

- Ya fadi hakan ne a garin Lokoja

- Yace zai fara ne da farfado tattalin arzikin Najeriya

Daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugabancin kasar nan ta Najeriya a zaben 2019 mai zuwa a jam'iyyar adawa ta PDP Sanata David Mark yayi alkawarin gyra Najeriya cikin shekaru biyu kacal idan ya zama shugaban kasa.

Zan gyara Najeriya cikin shekaru 2 kacal - Wani dan takarar shugaban kasa
Zan gyara Najeriya cikin shekaru 2 kacal - Wani dan takarar shugaban kasa
Asali: Facebook

KU KARANTA: An gano inda Nnamdi Kanu ya sulale

Sanata Mark dake zaman tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya yayi wannan ikirarin ne a ranar Talatar da ta gabata a garin Lokoja, babban birnin jihar Kogi lokacin da yake tattaunawa da masu ruwa da tsakin jam'iyyar a jihar.

Legit.ng ta samu cewa fitaccen dan siyasar wanda ya fito daga jihar Benue dake a shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya ya bayyana cewa cikin shekaru biyu na farkon wa'adin mulkin sa idan ya samu nasarar zama shugaban kasa zai farfado da tattalin arzikin kasar.

A wani labarin kuma, Wani binciken da aka gudanar yana nuni ne da cewa akalla mutane 123 ne suka sayi fom din neman tikitin takarar gwamna a jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya a zaben gama gari da za'a gudanar a shekarar 2019.

Mun samu wadannan alkaluman ne daga wata majiyar mu a babbar hedikwatar jam'iyyar ta PDP dake a garin Abuja bayan da aka sanar da rufe saida fom din a satin da ya gabata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel