Baja-baja: Ku karanta ku ga yawan kudin da jam'iyyar PDP ta tara daga sayar da fom din takara

Baja-baja: Ku karanta ku ga yawan kudin da jam'iyyar PDP ta tara daga sayar da fom din takara

- Naira miliyan 156 daga 'yan takarkarin su 13 na shugaban kasa

- Naira miliyan 728 daga 'yan takara 123 na gwamnonin jahohi

Yayin da ake kara kurewa zabukan gama gari a Najeriya, a bisa al'ada jam'iyyu sukan fitar da fom na 'yan takarar dake sha'awar tsayawa zabe a karkashin su akan wani kayyadajen farashi.

Baja-baja: Ku karanta ku ga yawan kudin da jam'iyyar PDP ta tara daga sayar da fom din takara
Baja-baja: Ku karanta ku ga yawan kudin da jam'iyyar PDP ta tara daga sayar da fom din takara
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya tayi taro kan karin albashi

A wannan zabukan na 2019 ma bata canza zani ba domin kuwa jam'iyyun sun fitar da fom din kuma an samu 'yan takarkari da dama a kuma dukkan matakai tun daga shugaban kasa zuwa 'yan majalisar jiha.

Legit.ng ta samu cewa duk da arhar fom din na babbar jam'iyyar adawa ta PDP musamman idan aka kwatanta da farashin fom din jam'iyyar dake mulki ta APC, jam'iyyar adawar ta tara kudi masu yawan gaske.

Wani bincike da mukayi akan yawan kudin da jam'iyyar ta samu a wurin 'yan takarar shuganan kasa kadai mun samu cewa sun kai yawan Naira miliyan 156 daga 'yan takarkarin su 13 da kowa ya biya Naira miliyan 12.

Haka zalika suma 'yan takarar gwamnoni a jam'iyyar sun tara jumlar Naira miliyan 728 daga 'yan takara 123 inda kowa ya biya Naira miliyan 6.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel