Yanzu Yanzu: Gwamnan jihar Kano ya rantsar da sabon mataimakin gwamna

Yanzu Yanzu: Gwamnan jihar Kano ya rantsar da sabon mataimakin gwamna

Gwamna Abdullahi Ganduje ya rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Nasiru Yusuf-Gawuna a ranar Laraba, 19 ga watan Satumba.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa an gudanar da taron rantsar da mataimakin gwamnan ne a gidan gwamnatin Kano, inda ya samu halartan dubban magoya baya.

Legit.ng ta tattaro cewa gwamnan yayi kira ga sabon mataimakinsa da ya zamo mai gaskiya da amana, da kuma jajircewa wajen gudanar da ayyukansa.

Gwamnan yace Yusuf Gawuna zai kama aiki da kwarewa da kuma gaskiya.

Yanzu Yanzu: Gwamnan jihar Kano ya rantsar da sabon mataimakin gwamna
Yanzu Yanzu: Gwamnan jihar Kano ya rantsar da sabon mataimakin gwamna
Asali: Depositphotos

Ya sanar da cewar sabon mataimakin gwamnan zai cigaba da aiki a matsayin kwamishinan gona, matsayin da yake riko a gwamnati kafin nadin nasa.

Mataimakin babban alkalin jihart, Justis Nura Sagir ne ya rantsar da mataimakin gwamnan.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar yan Najeriya dake zaune a kasar Amurka sun bukaci a bari su biya kudinfansar Leah Sharibu

A baya Legit.ng ta tattaro cewa Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai zamo jarumi kamar Ghandi, Mao Zedong da Mandela da irin wannan goyon baya da yake samu daga yan Najeriya da kuma tsarin siyasar jam’iyyar APC.

“Abunda ke faruwa a APC a yanzu zai yi mana kyau. Muna cire bara gurbi sannan muna samun tsarkaku a matsayin jam’iyyar siyasa. Muna gina jam’iyya da tunani mai tsari sannan muna da shugaba mai hangen nesa (Buhari), wadda zai kawo chanji mai aminci,” inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel