Matakan tantance dan takara a zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC

Matakan tantance dan takara a zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC

A ci gaba da fuskantar zaben fitar da gwani da jam'iyyun siyasa na kasar nan ke yi, kamar dai yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayar da umarni. Jam'iyyar APC ta fitar da jadawalin matakan da za ta bi wajen tantance yan takara a zaben fitar da gwani na jam'iyyar.

Jam'iyyar wacce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban jam'iyyar na kasa Comrade Adams Aliyu Oshiomhole da sakataren jam'iyyar na kasa Hon. Mai Mala Buni, ta bayyana cewa kwamitin gudanarwar jam'iyyar na kasa ne ya amince da tantance yan takarar da suka mayar da fom din nuna sha'awarsu ta tsayawa takara.

KARANTA WANNAN: Dokar haramta saki uku a lokaci guda ta soma aiki a India

Shugaban jam'iyyar APC na kasa Comrade Adams Oshionmohle
Shugaban jam'iyyar APC na kasa Comrade Adams Oshionmohle
Asali: Depositphotos

Ga jadawalin matakan tantance yan takarar jam'iyyar APC a zaben fitar da gwani.

 • Za a tantance masu sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa a birnin tarayya Abuja.
 • Za a tantance masu sha'awar tsayawa takarar gwamnoni, Sanatoci, da yan majalisun tarayya a babban birnin tarayya Abuja.
 • Za a tantance masu sha'awar tsayawa takarar majalisun dokoki, a jihohin su.
 • Za a fara tantance yan takarar a ranar Alhamis 20 ga watan Satumba, 2018, a kammala a ranar Asabar 22 ga watan Satumba, 2018, inda za a fara da misalin karfe 9 na safiyar kowace rana.
 • Kowace shiyya za a kafa kwamitin tantance Gwamnoni, Sanatoci da yan majalisun tarayya.
 • An zabi otel din Transcorp Hilton da Sharaton da ke Abuja a matsayin wuraren da za a gudanar da tantancewar.
 • Za a tantance yan takara da suka fito daga Arewa-maso-Gabas, Kudu-maso-Gabas da na Kudu-maso-Yamma, a otel din Transcorp Hilton da ke Abuja.
 • Za a tantance yan takara da suka fito daga Arewa ta tsakiya, Arewa-maso-Yamma, da kuma Kudu-maso-Kudu, a otel din Sharaton da ke Abuja.
 • An bukaci yan takara su tuntubi babban sakatariyar jam'iyyar ta kasa da ke Abuja don karin bayani akan lambobin waya kamar haka:
 1. Sakataren gudanarwa na kasa - 08033387484
 2. Daraktan tsare tsare - 08033481049
 3. Daraktan sashen ma'aikata - 08033801097

A baya bayan nan Legit.ng ta ruwaito maku cewa jam'iyyar APC ta sake daga ranar da zata gudanar da zabe zuwa ranar Talata 25 ga watan Satumba.

Sakataren gudanarwa na jam'iyyar na kasa Emmanuel Ibeduro, ya sanar da sauya lokacin a cikin wata sanarwa a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Bidiyo: Matsayar Ibrahim Babangida akan kudurin Saraki na shugabancin Nigeria | Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

Online view pixel