Dokar haramta saki uku a lokaci guda ta soma aiki a India

Dokar haramta saki uku a lokaci guda ta soma aiki a India

- Gwamnatin kasar India ta sanya dokar haramtawa maza furta kalmar saki uku a lokaci daya

- Gwamnatin India ta yi amfani da karfin ikon da kundin mulkin kasar ya bata, wajen tabbar da kudurin ya zama doka

- Daga cikin abubuwan da dokar ta kunsa, akwai hukuncin daurin shekaru 3 ga duk musulmin da ya karya dokar

Fira Ministan kasar India, Mr. Narendra Modi, ya amince tare da rattaba hannu kan sabuwar dokar da ta haramtawa musulmai furta kalmar saki uku a baki ko a rubuce, a lokaci daya.

A watan Augusta, Legit.ng ta ruwaito maku yadda sashen zartaswa na kasar ya aikewa zauren majalisar ta India da kudirin dokar haramtawa maza musulmi yiwa matansu saki uku a lokaci daya.

Sai dai a wancan watan, kudurin ya kasa wuce gaban majalisar, kasancewar bai samu karbuwa a wajen yan majalisun ba.

Dokar haramta saki uku a lokaci guda ta soma aiki a India
Dokar haramta saki uku a lokaci guda ta soma aiki a India
Asali: Getty Images

Biyo bayan kin amincewar majalisar zartaswa na wannan kuduri, ya sa gwamnatin kasar ta India ta yi amfani da karfin ikon da kundin mulkin kasar ya bata, wajen tabbar da kudurin ya zama doka, dokar ta gwamnatim ta ce zata fara aiki ba bata lokaci ba.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Ta tabbata Adeleke ya zana jarabawar WAEC a 1981

Daga cikin abubuwan da dokar ta kunsa, akwai hukuncin daurin shekaru 3 ga duk wani musulmi da aka kama da laifin yiwa matarsa saki uku a lokaci daya, tare da biyan tara.

A farkon shekara ta 2017, Fira Ministan India Narendra Modi, ya baiwa mata kariya kan hakkokinsu na aure ta hanyar bullo da wani sabon kuduri, sai dai shima wannam kudurin ya sha ruwa a gaban majalisar, bayan gaza samun rinjaye a amincewar yan majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel