Lagas na daga cikin birane mafi datti a duniya – Ma'aikatar kula da bola

Lagas na daga cikin birane mafi datti a duniya – Ma'aikatar kula da bola

- Hasashe shun nuna cewa jihar Lagas na daga cikin birane mafi datti a duniya

- Mataimakin shugaban AWAM yace hakan ya faru ne sanadiyar yunkurin da akeyi na hana ma’ikatan bolan yin aikinsu

- Yace mika ragamar aikin ma’aikatan kula da shara ga wata kamfanin kasar waje da Ambode yayi a 2016 ne ya haddasa rashin ba fannin cikakken kula

Kungiyar kula da bola na Najeriya wacce aka fi sani da Public Private Participation, tace jihar Lagas ta zamo daya daga cikin birane mafi datti a duniya.

Mataimakin shugaban AWAM, Mista David Oriyomi, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, 18 ga watan Satumba a Lagas yayinda yake zantawa da manema labarai yace birnin ta zamo mafi datti ne sakamakon yunkurin da akeyi na hana ma’ikatan sharan yin aikinsu.

Lagas na daga cikin birane mafi datti a duniya – Ma'aikatar kula da bola
Lagas na daga cikin birane mafi datti a duniya – Ma'aikatar kula da bola
Asali: Depositphotos

Oriyomi, ya bayyana cewa kaddamar da shirin Cleaner Lagos Initiative a 2016 da Gwamna Akinwumi Ambode yayi tare da kudirin ba kamfanin kasar waje mai suna “Visionscape” kula da ragamar aikin karban sharan ita kadai daga hannun 350 PSP, ne ya haddasa lamarin rashin bin ka’idan kula da sharan bolan.

A cewarsa hakan ya zoma AWAM a bazata domin babu wani tuntuba da akayi masu.

KU KARANTA KUMA: APC ta shirya makarkashiya don tsige Saraki da Dogara – CUPP

A baya munji cewa rahoton gidauniyar Bill and Melinda Gates na shekara, ta bayyana cewa Najeriya zata kasance da mutane mafi talauci a duniya a 2050.

A cewar shafin gidauniyar na yanar gizo, rahoton yayi duba ga nasarorin da aka samu a fadin duniya. A wannan shekarar, daga taron har rahoton zai mayar da hankali akan yawan matasa da zasu shafi cigaban duniya anan gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng