Bakar uwa: Wata mata ta sayar da yaronta akan N350,000 don ta yi shagalin kirsimeti da kudin

Bakar uwa: Wata mata ta sayar da yaronta akan N350,000 don ta yi shagalin kirsimeti da kudin

- Wata mata, Oluchi Mba ta sayar da yaronta mai shekaru 7 da hauhuwa akan kudi N350,000.

- Rundunar yan sanda ta ce wadanda ake zargin an cafke su, tare da cewar an kwato yaron daga hannun su.

- Rundunar ta ce za a gurfanar da masu laifin gaban kotu da zaran an kammala bincike

Rahotannin da Legit.ng ta samu ata mata mai shekaru 28 da ke da zama a Ogidi, karamar hukumar Idemili ta Arewa, jihar Anambra, Oluchi Mba ta sayar da yaronta mai shekaru 7 da hauhuwa akan kudi N350,000.

Legit.ng ta tattara rahoton cewa, Mba ta yanke wannan hukunci ne a kokarin da ta ke yi na tara kudin da zata yi shagalin bikin kirismeti na wannan shekarar, wanda ya sa ta sayar da yaron nata mai shekaru 7 da hauhuwa akan N350,000.

Wata majiya ta labarta yadda matar ta ke ta dokin zata yi shagalin kirismetin na wannan shekarar a watanni uku masu zuwa cikin wadatar kudi, kafin daga bisani yan sanda su cafke ta.

Bakar uwa: Wata mata ta sayar da yaronta akan N350,000 don ta yi shagalin kirsimeti da kudin
Bakar uwa: Wata mata ta sayar da yaronta akan N350,000 don ta yi shagalin kirsimeti da kudin
Asali: UGC

KARANTA WANNAN: Attahiru Bafarawa: Ni na rike hannun Buhari na sanya shi cikin harkokin siyasa

"Muna tare a ranar lahadi inda ta ke ta dokin yadda zata kashe kudi wajen bikin kirsimeti na wannan shekarar

"Na shaida mata cewa kamar ta yi gaggawar fara shirin bikin, ganin cewa akwai watanni uku kafin ranar tanzo, amma duk da haka bata daina wannan doki ba. Sam ban san cewa tana shirin sayar da yaronta bane," a cewar majiyar.

Rahotanni sun bayyana cewa Mba ta saida yaron ne ga wata mata mai shekaru 55, Edith Obiakor, da ke zama a layin Akudo a garin Nkpor.

Da aka tsananta bincike, sai aka gano cewa ita ma Obiakor, ta sake sayar da yaron ga surukinta mai suna Vitus Aniunoh, da ke zama a layin Patterson, garin Fegge a Onitsha, akan N650,000.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda na jihar, Haruna Mohammed, ta tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu.

Ya ce wadanda ake zargin an cafke su, tare da cewar an kwato yaron daga hannun su.

Mohammed ya ce za a gurfanar da masu laifin gaban kotu da zaran sun kammala bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel