Cikin shekaru 3: Mun tsamo yan Nigeria Miliyan 10 daga talauci - Gwamnatin Buhari

Cikin shekaru 3: Mun tsamo yan Nigeria Miliyan 10 daga talauci - Gwamnatin Buhari

- Gwamnatin tarayya ta bugi kirji da cewar ta tsamo yan Nigeria Miliyan 10.073 daga kangin talauci zuwa wadatar arziki

- Daga cikin shirye shiryen gwamnatin na samarwa tsamo yan Nigeria daga talauci akwai shirin ciyar da dalibai da shirin bada 5,000 ga marasa karfi

- Akwai shirye shiryen N-Power, Anchor Borrowers, da kuma bada bashin 10,000 zuwa 50,000 ga yan kasuwa masu karamin karfi

Ministan kasafi da tsarin kudi na kasa, Sanata Udoma Udo Udoma, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta tsamo yan Nigeria 10.073 daga kangin talauci zuwa wadatar arziki. Ya bayyana hakan ne a wani taron shirye shiryen babban taron tattalin arzikin Nigeria karo na 24 mai take (NES#24).

Sanata Udoma ya ce gwamnatin tarayya ta dauki matakai don tsamo yan Nigeria miliyan 10 daga talauci zuwa wadatar arziki, daga cikin manyan hanyoyin farfado da tattalin arzikin kasar da kuma kiddigar arzikin kasa ERGP.

A cewar sa, ta ce ta bunkasa rayuwar daliban makarantun firamare miliyan 8.96 ta hanyar shirin ciyar da dalibai abinci; sama da talakawa 297,000 da marasa galihu ta hanyar tallafin N5,000 a kowane wata; rabawa sama da mutane 308,000 bashin N50,000 da kuma bunkasa rayuwar matasan da suka kammala karatu ba aiki 200,000 ta hanyar shirin N-Power, yayin da aka zabi wasu 308, 000 don amfana da shirin karo na biyu.

KARANTA WANNAN: Ya zamarwa Pogba wajibi ya koyi darasi daga Cristiano Ronaldo - Rio Ferdinand

Ministan kasafi, Sanata Udoma Udo Udoma
Ministan kasafi, Sanata Udoma Udo Udoma
Asali: Depositphotos

Ministan ya ce gwamnati ta kuma inganta fannin noma ta hanyar raba bashin Naira Biliyan 82 ga manoma 350,000 a karkashin shirin Anchor Borrowers, tare da gina kamfanoni 14 na sarrafa takin zamani da kuma shirin samar da taki na shugaban kasa, wanda ya samar da tan Miliyan 2.3 na takin NPK.

A cewar ministan, taron (NES#24) zai karkatane kan samar da nagartacciyar gwamnati da zata bunkasa tattalin arzikin kasar, tare da gano hanyoyin dakile dukkanin matsalolin da fannin tattalin ke fuskanta da ma wanda zai iya fuskanta a nan gaba.

Kungiyar shirya taron tattalin arziki ta Nigeria tare da hadin guiwar gwamnatin tarayya ne ke shirya taron a kowace shekara wanda ke samun wakilcin ma'aikatar kasafi da tsare tsaren kudade na kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Yadda Okezie Ikpeazu ya bunkasa jihar Abia | Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

Online view pixel