Ya zamarwa Pogba wajibi ya koyi darasi daga Cristiano Ronaldo - Rio Ferdinand

Ya zamarwa Pogba wajibi ya koyi darasi daga Cristiano Ronaldo - Rio Ferdinand

- Rio Ferdinand, ya ce akwai bukatar Paul Pogba ya yiwa kansa karatun ta-nutsu ta hanyar koyon darasi daga Cristiano Ronaldo

- Ana zargin Pogba da maida hankali ga son kanshi, mai makon mayar da hankali kan buga wasa mai kyau da zai baiwa Man United nasara

- A na sa ran Pogba zai buga tsakiya a wasan da United za ta yi da Young Boys a wasan cin kofin zakarun turai da zasu buga a mako mai zuwa

Tsohon dan wasan Manchester United, Rio Ferdinand, ya ce akwai bukatar Paul Pogba ya yiwa kansa karatun ta-nutsu ta hanyar koyon darasi daga Cristiano Ronaldo, duba da cewar ya canja sosai sabanin lokacin da zo Man United.

Pogba na ci gaba da samun kalubale a Old Trafford saboda rashin samun wani kyakkyawan sakamakon a dukkanin wasannin da kungiyar kwallon kafar ta ke bugawa da shi, musamman wasan da ya buga da kasar Faransa da Rasha a 2018.

Ana zargin sa da maida hankali ga son kanshi, ta yadda duniya zata kalle shi mai makon mayar da hankali kan buga wasa mai kyau da zai baiwa Man United nasara, sannan bayan bulluwar jita jitar cewa dan wasan mai shekaru 25 yana kokarin komawa Barcelona, Ferdinand ya ce Pogba baya kallon Old Trafford a matsayin gida a gareshi.

KARANTA WANNAN: 2019: PDP a jihar Legas ta tsaida Saraki a matsayin dan takarar shugaban kasa

Ya zamarwa Pogba wajibi ya koyi darasi daga Cristiano Ronaldo - Rio Ferdinand
Ya zamarwa Pogba wajibi ya koyi darasi daga Cristiano Ronaldo - Rio Ferdinand
Asali: Getty Images

Ferdinand ya buga misali da tsohon dan wasan Man United, Cristiano Ronaldo, wanda ya samu horon taka ledarsa a Red Devils, inda a yau ya zama zakaran gwajin dafi a duniya, wanda ya lashe kambun zakaran dan wasa na Ballons d'Or har sau biyar.

A cewar Rio Ferdinand, ya zamarwa Paul Pogba wajibi ya yiwa kansa karatun ta-nutsu tare da bin kafar Cristiano Ronaldo.

Sai dai Ferdinand na ganin cewa mai horas da yan wasa na Manchester United, Jose Mourinho na da muhimmiyar rawar da zai taka wajen gyara fasalin Pogba don ganin cewa ya zama wani abu a duniyar wasan taka leda ta hanyar karfafa shi a bangaren da ya fi kwarewa.

A na sa ran cewa Pogba zai buga tsakiya a wasan da United za ta yi da Young Boys a kakar cin kofin zakarun turai da zasu buga a mako mai zuwa, wanda shi ne karo na farko da suka fara buga wasa a wajen gida bayan buga wasanni 5 na Firimiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Cinikayyar yan wasa: Yan wasan da suka cancanci milyoyin kudi | Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng