Dan majalisa ya goyi bayan tazarcen Buhari da motoci 100

Dan majalisa ya goyi bayan tazarcen Buhari da motoci 100

Dan majalisar wakilai mai wakiltan yankin Chanchaga, Umar Bago yace zai goyi bayan tazarcen Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Abbakar Bello na jihar Niger da motoci 100.

Bago wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, 18 ga watan Satumba a hira da kamfanin dillancin labarai a Minna ya bayyana cewa shugabannin biyu sune zabin jama’ar Niger a zaben 2019.

Ya bukaci masu zabe da su zabi ci gaba domin a cigaba a tafiyar chanji da zai hau da kasar Najeriya kan tsanin inganci.

Dan majalisa ya goyi bayan tazarcen Buhari da motoci 100
Dan majalisa ya goyi bayan tazarcen Buhari da motoci 100
Asali: UGC

Bago ya bayyana cewa motocin zai ba jami’an APC da sauran hukumomin wajen ganin nasarorin da Buhari da Bello suka samu.

KU KARANTA KUMA: Zan cigaba da yin adalci wajen nade-nade na – Buhari yayi alkawari

Yace a shekaru uku da yan watanni da gwamnatin APC tayi tana mulki, shugabannin biyu sun nuna tsarin shugabanci mai kyau kuma mutanen Nigeriya da jihar Niger na alfahari da su.

A cewar Bago wannan shine gudunmawarsa ga shugabanin biyu da suka nuna kyakyawar jakadanci na jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku neme mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel