Kotu ba da belin malamin jami’ar da ke kwana da maza a kafin su ci jarabawar sa

Kotu ba da belin malamin jami’ar da ke kwana da maza a kafin su ci jarabawar sa

Wata kotu dake da zama a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo ta gurfanar da wani malamin jami’ar koyar da ayyukkan gona dake jihar mai suna Aremu Olufemi bisa zargin laifin aikata madugo da dalibansa maza.

Lauyan da ke kara Mathew Ojeah ya sanar da cewa Olufemi mazaunin layin Olugbode ne a unguwar Odo-Ona dake garin Ibadan na tursasa dalibansa kwana da shi ko kuma su fadi jarabawarsa.

A cewarsa: “Idan daliban sa suka zo neman ba’asi kan yadda aka yi suka fadi jarabawaru sai Olufemi ya nemi sabuwar wayar tarho mai suna Infinix Hot note IV daga wajen su.”

Ojeah yace a lokacin da dalibi zai kawo masa wayar da ya bukata ne sai ya nemi kwana da shi.

Kotu ba da belin malamin jami’ar da ke kwana da maza a kafin su ci jarabawar sa
Kotu ba da belin malamin jami’ar da ke kwana da maza a kafin su ci jarabawar sa
Asali: Facebook

Ya kuma kara da cewa wannan bashi bane karo na farko ba da Olufemi ke aikata irin wannan ta’asar ba saboda kuwa akwai wani dalibi mai suna Jamiu Lateef da ya yi karansa.

Yayin da yake kare kan sa Olufemi ya musanta aikata haka a kotun sannan lauyan dake kare shi J.A. Apo ya nemi kotu da ta bada belin Olufemi.

A halin da ake ciki mai shari'a a kotun Jejelola Ogunbona ya bayar da belin wanda ake zargin a kan naira 50,000 tare da gabatar da shaida guda daya.

Za a ci gaba da sauraron shari'an a ranar 19 ga watan Oktoba.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Fasto Amos Olugbenga na cocin Christ Kingdom, Ilorin yayi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su sanya dokar da zai yi duba ga shigar banga a kasar.

KU KARANTA KUMA: Maye gurbin Adeosun da Zainab Ahmad: Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta caccaki Buhari

Olugbenga yayi kiran ne a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Ilorin a ranar Talata, 18 ga watan Satumba.

Legit.ng ta tattaro cewa ya lura cewa shigar banza ya zamo ruwan dare a tsakanin matasa a kasar, cewa hakan na dakushe al’adu da martaban kasar daga zukatan yaran zamani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel