Zan sauya fasalin Najeriya idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa – Attahiru Bafarawa

Zan sauya fasalin Najeriya idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa – Attahiru Bafarawa

- Tsohon gwamnan Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bukaci wakilan jam’iyyar sa ta PDP da su zabe shi a matsayin dan takaransu

- Bafarawa ya sha alwashin chanja fasalin lamuran kasar idan har aka zabe shi a matsayin sugaban kasa a 2019

- Tsoon gwamnan dai ya kasance daya daga cikin masu neman tikitin tsayawa takaran shugaban kasa a zabe mai zuwa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar kujeran shugaban kasa a zabe mai zuwa, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bukaci wakilan jam’iyyar sa ta PDP da su zabe shi a zaben fitar da gwani da za a yi ranar 5 da 6 ga watan Oktoba.

Bafarawa yaba da tabbacin cewa idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya toh zai chanja fasalin lamuran kasar ta yadda babu wani yanki da zai fito yana korafin an mai dashi saniyar ware.

Zan sauya fasalin Najeriya idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa – Attahiru Bafarawa
Zan sauya fasalin Najeriya idan aka zabe ni a matsayin shugaban kasa – Attahiru Bafarawa
Asali: Depositphotos

Da ya ke zantawa ga wakilan PDP a garin Akure, babban birnin jihar Ondo, Bafarawa ya yi kira ga wakilan da su zabe shi domin gwamnatin sa za ta inganta rayuwar talakawan Najeriya sannan ta saita tare da inganta tattalin arzikin kasar.

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Gombe kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party’s (PDP), Ibrahim Dankwambo ya nuna jajircewarsa na son kawo karshen duk wani kashe-kashe na kabilanci da addini a fadin kasar, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 2019.

Dankwambo ya bayyana hakan a wata sanarwa da sanya hannun Dr Ayoade Adewopo, daraktan labarai na kungiyar kamfen dinsa a Abuja a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Zuciyana na tare da Buhari tun a 2015 – Sanata Akpabio

Gwamnan yayi jaje ga wadanda harin kauyukan Gon, Nzumosu, Bolki, Nyanga da Bukuto dake karamar hukumar Numan na jihar Adamawa ya cika dasu, inda aka kashe malami da wasu mutane 51.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel