Asirin Obasanjo ya tonu: An bankado badakalarsa a kamfanin NNPC na tsawon shekaru 8

Asirin Obasanjo ya tonu: An bankado badakalarsa a kamfanin NNPC na tsawon shekaru 8

- A cewar wani sabon littafi Obasanjo ya shugabanci kamfanin NNPC shi daya "Tilo" har na tsawon shekaru 8

- Tsohon shugaban kasar bai tafa tattauna bayanan kamfanin na NNPC da wani jami'i na gwamnatinsa ba

- Littafin ya bayyana kulla kullar da yayi har ya zama ministan man fetur a cikin kankannin lokaci, a wani taro na majalisar zartaswa ta kasar

Bisa rahotannin da Legit.ng ta tattara, daga wani sabon littafi da aka wallafa, ta gano cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya shugabanci kamfanin samar da mai na kasa NNPC a matsayin shugaban kamfanin "Tilo" har na tsawon shekaru 8 da ya shugabanci kasar.

A cewar lottafin mai suna 'Too Good to Die: Third Term and the Myth of the Indispensable Man in Africa’, ya bayyana cewa a lokacin da ya ke a matsayin ministan man fetur, tsohon shugaban kasar bai tafa tattauna bayanan kamfanin na NNPC da wani jami'i na gwamnatinsa ba.

Obasanjo, wanda ya kasance a matsayin shugaban kasa daga 1999 zuwa 2007, ya nasa kansa ministan da zai kula fannin mai na kasar, har zuwa watan Janairu 2007, a lokacin ne ya sauka daga mukamin.

Jami'in gwamnati daya ne Obasanjo ya ke kulla makircinsa da shi , Edwund Daukoru, mai bashi shawara kan man fetur da makamashi, wanda ya ba ministan albarkatun man fetur a 2005.

KARANTA WANNAN: Akalla mutane 2,700 ne suka sauya sheka daga APC zuwa PDP a birnin tarayya Abuja

Asirin Obasanjo ya tonu: An bankado badakalarsa a kamfanin NNPC na tsawon shekaru 8
Asirin Obasanjo ya tonu: An bankado badakalarsa a kamfanin NNPC na tsawon shekaru 8
Asali: Instagram

A cikin littafin wanda marubuci Chidi Odinkalu, tsihon shugaban hukumar kare hakkin dan adam NHRC, tare da Ayisha Osori, mawallafiyar littafin 'Love Does Not Win Elections', suka taru suka wallafa, littafin ya ce Obasanjo ne ke yanke duk wani hukunci na gudanar da ayyukan fannin man fetur a kasar.

Sun bayyana kulla kullar da yayi har ya zama ministan man fetur a cikin kankannin lokaci, a wani taro na majalisar zartaswa ta kasar.

Marubutan sun wallafa cewa: "A wani taron aiki na karshe da majalisar zartsawa a watan Mayu, 2007, Obasanjo ya bukaci mahukuntan da su amince masa ya zama ministan man fetur na tsawon shekaru 8 da ya kwashe yana shugabantar kamfanin NNPC shi daya 'tilo'.

Abin mamakin shine, a lokacin da Obasanjo ya ke shugaban kasa a mulkin soja, a 1977, ya kafa wani kwamitin bincike kan harkokin kamfanin man fetur na kasa mai suna NNOC a wancen lokaci, kafin daga bisani aka mayar da shi NNPC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel