Ta-leko-ta-koma: Mataimakin kakakin majalisar wakilai ya ce bai koma PDP ba

Ta-leko-ta-koma: Mataimakin kakakin majalisar wakilai ya ce bai koma PDP ba

- Mataimakin kakakin majalisar wakilai ya ce bai koma PDP ba

- Yace yana nan daram a jam'iyyar APC

- Sunan sa Honorabul Yussuf Lasun daga jihar Osun

Mataimakin kakakin majalisar wakilai a tarayyar Najeriya mai suna Honorabuk Yussuf Lasun a ranar Lahadin da ta gabata ya fito karara ya bayyanawa duniya shi har yanzu yana nan jam'iyyar sa ta All progressives Congress (APC).

Ta-leko-ta-koma: Mataimakin kakakin majalisar wakilai ya ce bai koma PDP ba
Ta-leko-ta-koma: Mataimakin kakakin majalisar wakilai ya ce bai koma PDP ba
Asali: Instagram

KU KARANTA: An tsinci gawar Manjo Janar Alkali da ya bace

Wannan dai kamar yadda muka samu, na zaman tamkar martani ga labaran da suka yi ta yawo a kwanakin baya na cewa mataimakin kakakin majalisar ta tarayya ya koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Legit.ng dai haka zalika ta samu cewa wannan dambarwa dai ta siyasa da kuma matsayar ta mataimakin kakakin majalisar na zaman tamkar wata koma baya ga babbar jam'iyyar adawa ta kasar a kokarin da takeyi na ganin ta rinjaye a majalisar.

Shi dai Honorabul Lasun kamar yadda muka samu yana wakiltar mazabar Irepodun/Olorunda/Orolu/Osogbo ne a majalisar tarayyar daga jihar Osun kuma ana zargin cewa akwai kyakkyawar alaka tsakanin sa da kakakin majaisar Yakubu Dogara da tuni ya sauya sheka zuwa PDP.

A wani labarin kuma, A wani yanayi dake zaman karon farko tun bayan korar sa daga mukamin sa na babban Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya da Shugaba Buhari yayi a watannin baya, Injiniya Babachir Lawal yayi magana da 'yan jarida a karon farko.

Shi dai tsohon Sakaten gwamnatin tarayyar, ya bayyana cewa ko kusa shi korar da Shugaba Buhari yayi masa daga gwamnatin sa a watannin baya ma shi gaba ta kai shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel