Wata babbar kotun Ikeja ta yankewa wasu yan ta'adda 2 hukuncin shekaru 42 a gidan wakafi

Wata babbar kotun Ikeja ta yankewa wasu yan ta'adda 2 hukuncin shekaru 42 a gidan wakafi

- Wata babbar kotu da ke Ikeja, ta garkame wasu gaggan masu garkuwa da mutane guda 2, a gidan kaso na tsawon shekaru 41

- Wadanda aka yankewa hukuncin, na daga cikin tawagar kasurgumin dan ta'addan nan Chukwudimeme Onwuamadike, da aka fi sani da Evans

- An yanke masu hukuncin zuwa gidan kurkuku, bisa aikata laifukan cin amanar kasa, garkuwa da mutane da kuma fashi da makami

Mai shari'a Oluwatoyin Taiwo na wata babbar kotu da ke Ikeja, ya yanke hukunci shekaru 41 a gidan kaso ga wasu gaggan masu garkuwa da mutane guda biyu, wadanda tsofaffin yarane ga wani kasurgumin mai garkuwa da mutane ta Chukwudimeme Onwuamadike, da aka fi sani da Evans.

Wadanda aka yankewa hukuncin: Kelvin Emenike Ukoh, 32 da kuma Emaka Obasi, 33, an yanke masu wannan hukunci na zaman wakafi bisa aikata laifin garkuwa da wani jami'in safarar kaya ta jirgin ruwa, Mr Ugoje Judge, da ma'aikaciyarshi, Miss Piriye Gogo a ranar 3 ga watan Augusta, 2012, ta'addancin da shugabansu na da Evans ya jagoranta.

A shekara ta 2013, an taba gurfanar da masu laifin taee da wasu guda 3: Uche Ighani, 28 Chibuzor Osuagwu, 33 da kuma Onowu Ngozi 3y, bisa aikata laifuka 14, da suka hada da cin amanar kasa, garkuwa da mutane, fashi da makami da kuma kisan kai.

KARANTA WANNAN: Cakwakiya: Wata kotu ta aikewa da Bukola Saraki sammaci game da fashin bankunan Offa

Wata babbar kotun Ikeja ta yankewa wasu yan ta'adda 2 hukuncin shekaru 42 a gidan wakafi
Wata babbar kotun Ikeja ta yankewa wasu yan ta'adda 2 hukuncin shekaru 42 a gidan wakafi
Asali: UGC

Legit.ng ta taba ruwaito cewa kasurgumin dan ta'adda Evans da tawagarsa sun sace wata daraktar Ocean Glory, Mr. Paul Cole, tare da janar manajanshi, Mr Jude Ugoje, da kuma daya daga cikin ma'aikatanshi, Piriye Gogo, a ranar 3 ga watan Augusta, 2012, inda aka boyesu a wani wajen da babu wanda ya sani.

Da ta ke bada labarin yadda ta kaya a waccen rana, Miss Gogo ta ce sun shuna masu bindiga a kan hanyarsu ta komawa gida, inda har suka so su yi mata fyade a cikin mota, amma jinin al'adar ta take yi ya hana su aikata hakan.

Mr Jude, wanda ya yi bayani a gaban kotu, ya ce wadanda suka yi garkuwa da shi sun bukaci ya biya Naira Miliyan 10 a matsayin kudin fansar sa, amma bayan dogon ciniki, suka amince da karbar Miliyan 5.

Mai shari'a Taiwo, bayan dogon nazari, ya yankewa Ukoh da Obasi, shekaru 5, 15 da 21 a gidan kurkuku, bisa aikata laifukan cin amanar kasa, garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel