Za’a fara sanya ruwan ganyen ‘Wiwi’ cikin Coca Cola

Za’a fara sanya ruwan ganyen ‘Wiwi’ cikin Coca Cola

Rahotanni sun nuna cewa Kamfanin Coca-Cola na kan tattaunawa da kamfanin ‘Wiwi’ na Aurora Cannabis, domin fara sanya ruwan ganyen Wiwi cikin abin sha.

Game da cewa BNN Bloomberg, kamfanin Coca-Cola wacce ita ce kamfanin kayan shaye-shaye mafi girma a duniya na shawaran sanya ruwan wiwi wato cannabidiol, cikin Coca Cola.

A wani wasika da kakakin BNN Bloomberg, Kent Landers, ya samu daga Coca-Cola, suka ce: “Tare da wasu kamfanoni, muna kokarin ganin yadda za’a sana ruwan ganyen wiwi cikin abubuwan sha a fadin duniya. Har yanzu dai bamu yanke wani shawara ba.”

Za’a fara sanya ruwan ganyen ‘Wiwi’ cikin Coca Cola
Za’a fara sanya ruwan ganyen ‘Wiwi’ cikin Coca Cola
Asali: Facebook

A wani wasikar daban daga kakakin Aurora, Keather McGregor, tace: “Doka ce a wajenmu ba mu bayyana kasuwancinmu har sai mun yanke shawara, amma muna da hakkin bayyanawa masu hannu jari irin damar da zasu samu.”

Wannan labari ya biyo bayan rahoton da muka kawo muku cewa kamfanin Coca-cola ta bayyana niyyar fara yin giya. Gabanin yanzu ana zargin kamfanin da sanya sinadarai cikin abin shanta wanda ke da illa ga cikin dan Adam.

Amma kasancewan kamfanin kasashen yahudu ne, ba'a samu galaba a kansu ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel