Kana da karfin zuciya – PDP ga Dogara yayinda ya dawo jam’iyyar
- PDP tayi wa Kakakin majalisa Yakubu Dogara maraba da dawowa tushen sa
- Kwanan nan Dogara ya sauya sheka daga APC zuwa tsohuwar jam’iyyarsa PDP
- PDP ta bayyana dawowar Dogara jam’iyyar a matsayin mataki mai karfin gwiwa
A ranar Lahadi, 16 ga watan Satumba, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi wa kakakin majalisar wakilai, Honourable Yakubu Dogara, sannu da zuwa tsohuwar jam’iyyarsa daga All Progressives Congress (APC).
PDP a wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan, a Abuja ta bayyana cewa dawowar Dogara martani ne ga kiran da jam’iyyar tayiwa masu kishin kasa don su hada kais u ceto kasar.
Ologbodiyan ya bayyana hukuncin Dogara naa sauya sheka daga APC a matsayin yunkuri da ya nuna cewa shi dattijo ne, wadda ke son ganin ci gaban kasar, musamman a wannan lokaci da take cikin mawuyacin hali.

Asali: UGC
Ya kara da cewa yunkurin Dogara buri ne na al’umman mazabarsa da kuma kiran yan Najeriya dake gangami a karkashin jam’iyyar don ganin PDP ta tsige gwamnatin APC.
KU KARANTA KUMA: Yayan APC sun yi ma gwamnan jahar Zamfara ruwan duwatsu a Gusau
Yace Dogara ya ci gaba da jajircewa wajen tafiyar da harkokin majalisa duk da kokarin karkatar da hankalinsa da jam’iyyar APC ke ta kokarin yi.
Ya bad a tabbacin cewa dawowar Dogara jam’iyyar na alamu ne na cewa PDP zata kafu sannan tayi nasara a jihar Bauchi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng