Wajibi ne Adeosun ta dawo da dukkan albashin da ta karba, kuma a gurfanar da ita - PDP

Wajibi ne Adeosun ta dawo da dukkan albashin da ta karba, kuma a gurfanar da ita - PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP ta ce ya kamata a wajabtawa tsohuwar minister kudi, Mrs Kemi Adeosun, wacce tayi murabus daga kujeran rana Juma’ar da ya gabata dawo da dukkan albashin da ta taba karba.

Jam’iyyar tace Kemi Adeosun ta dawo da kudaden tun lokacin da take kwamishana a jihar Ogun har lokacin da aka nadata minister kudi.

Bayan hakan, jam’iyyar adawar tace ya kamata hukuma ta tilasta Adeosun bayyana wadanda suka taimaka mata wajen samun takardan bautar kasa bogin da take amfani da shi.

Shugaba jam’iyyar PDP, Uche Secondus, yace a hira da manema labarai ranan Lahadi a birnin tarayya Abuja.

Yace idan Adeosun ta ambaci sunan wadanda suka taimkata mata, zai taimaka wajen rage irin wannan abin kunyan.

KU KARANTA: Babu wanda ya isa ya tsige ni – Saraki

Secondus ya kara da cewa murabus dinta bai isa ba, wajibi ne ta fuskanci fushin doka saboda hakan ya zama izina ga wasu.

Ya kara da cewa rashin daukan matakin da gwamnatin tarayya karkashin shugaba Muhammadu Buhari yaudarar mutane take da ikirarin yaki da rashawa.

Secondus yace: “Dubi ga yadda rashin gaskiya ke gudana a wanna gwamnatin, babu yadda minister za tayi murabus idan ba an zabe ya gabatowa.”

Tsohuwar minstar kudin Najeriya, Kemi Adeosun, ta yi murabus daga kujeranta bisa ga zargin amfani da kwalin bautar kasa wato NYSC na bogi. Jim kadan baya murabus ta gudu daga Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel