Dandalin Kannywood: Gaskiyar alaka ta da Adam A. Zango - Zainab Indomi

Dandalin Kannywood: Gaskiyar alaka ta da Adam A. Zango - Zainab Indomi

- Zainab Indomie ta fadi me ke tsakanin ta da Adam Zango

- Tace ya taimake ta sosai

- Tace ta dauke shi a matsayin dan uwa

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Zainab Abdullahi da aka fi sani da Zainab Indomie ta bayyana ainihin alakar ta da jarumi, Adam A. Zango.

Dandalin Kannywood: Gaskiyar alaka ta da Adam A. Zango - Zainab Indomi
Dandalin Kannywood: Gaskiyar alaka ta da Adam A. Zango - Zainab Indomi
Asali: Facebook

KU KARANTA: Auren jarumar fim ya mutu bayan wata 3

Jarumar dai wadda yanzu haka ta sanar da dawowar ta harkokin fina-finai ta ce ita ta dauki Adamu a matsayin ubangida a gare ta da har zata iya kiran sa dan uwa amma babu zancen soyayya a tsakanin su.

Zainab Indomie ta kara da cewa: "Zango ya na taimaka min sosai, musamman don ganin na cimma nasara a wannan sana'a".

Legit.ng ta samu cewa wannan dai na zuwa ne a lokacin da ake ta rade-raden cewa jaruman suna shirin yin aure ne sakamakon soyayyar dake tsakanin su musamman ma bayan da Adam Zango din ya saki matar sa.

Ita dai jaruma Zainab Indomie, kamar yadda masoya da masu sha'awar hrkokin fina-finan Hausa suka fi sanin ta, tauraruwar ta ta haska sosai tare da yi fice a tsakanin abokan sana'arta a shekarun baya musamman sakamakon irin rawar da ta taka a wasu manyan fina-finai.

Haka zalika jarumar ta lashe kyaututtuka da dama a lokacin tare kuma da fitowa a cikin fina-finai da dama da suka hada da Garinmu Da Zafi, Ali, Wali Jam da dai sauran su kafin daga baya rayuwar ta ta sururuce.

A kwanan baya dai jarumar ta ce ta shirya t dawowa harkar fina finai bayan shekaru da dama bayan bacewar fuskar ta.

Latsa wannan domin samun zafafan labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook a nan: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter a anan: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel