Wani dan takarar shugaban kasa ya roki 'yan Najeriya su siya masa fom din takara

Wani dan takarar shugaban kasa ya roki 'yan Najeriya su siya masa fom din takara

- Dan takarar shugaban kasa ya roki 'yan Najeriya su siya masa fom

- Yace a tara masa Naira miliyan 3 da dubu dari 5

- Sunan dan takarar Fela Durotoye

Daya daga cikin 'yan takarkarin kujerar shugaban kasar Najeriya a zabukan 2019 dake tafe mai suna Fela Durotoye, ya roki 'yan kasar da su taimaka masa su tattara masa kudin da zai sayi fom domin takarar tasa a jam'iyyar adawa ta Alliance for a New Nigeria (ANN).

Wani dan takarar shugaban kasa ya roki 'yan Najeriya su siya masa fom din takara
Wani dan takarar shugaban kasa ya roki 'yan Najeriya su siya masa fom din takara
Asali: Instagram

KU KARANTA: Yan kasuwa sun kunyata Gwamnan Kaduna

Mun samu cewa fom din takarar shugabancin kasar na jam'iyyar adawar dai ana saida shi ne akan Naira miliyan 3.5 wanda ya bayar da shawarar cewa da an samu mutane kadan da kowa ya bayar da Naira dubu daya to za a hada masa kudaden fom din.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa Mista Fela Durotoye ya kara da cewa dole ne 'yan Najeriya sai sun sadaukar da wani bangare na dukiar su da jin dadin su ne kadai sannan za su iya tabbatar da shugabanci na adalci.

A wani labarin kuma, Wasu 'yan Najeriya musamman ma daga bangaren kudancin kasar nan sun yi ta surutai da gungunai ga Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari game da sabbin nade-naden da ya yi a 'yan kwanakin nan.

Yan Najeriyar dai wadan da suka nuna rashin jin dadin su musamman ma a kafofin sadarwar zamani, sun bayyana nade-naden a matsayin babban rashin adalci da kuma tsantsar son kai daga bangaren na shugaban kasar da suka zarga da nada 'yan arewa kadai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel