Yanzu yanzu: Tsohon gwamnan jihar Osun ya yanke jiki ya fadi, an garzaya da shi asibiti

Yanzu yanzu: Tsohon gwamnan jihar Osun ya yanke jiki ya fadi, an garzaya da shi asibiti

- Rahotanni da muka samu na cewa an garzaya da tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja, asibitin UCH

- A cewar rahoton, ya yanke jiki ya fadi a wata ganawarsa da mambobin jam'iyyar ADC a Ibadan

- Wani daga cikin makusantansa da ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce nan bada dadewa ba za'a sallami tsohon gwamnan

Rahotannin da ke zuwa mana na cewa tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Rashidi Adewolu, ya yanke jiki ya fadi, inda aka garzaya da shi asibitin UCH da ke Ibadan, bisa lalurar da ba'a bayyana ba.

Wakilin Legit.ng da ke Ibadan, Newman Babson, ya bada rahoton cewa Ladoja wanda shi ne shugaban jam'iyyar ADC ta jihar, ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da taron duba hanyoyin samun nasarar jam'iyyar a zaben gwamnan jihar Osun, da za a gudanar mako mai zuwa.

Bisa tabbacin da Legit.ng ta samu daga waji makusancin shugaban, rashin lafiyar Rashidi ba mai tsanani ba ce, yana mai cewa nan bada dadewa ba za a salame shi.

Yanzu yanzun: Tsohon gwamnan jihar Osun ya yanke jiki ya fadi, an garzaya da shi asibiti
Yanzu yanzun: Tsohon gwamnan jihar Osun ya yanke jiki ya fadi, an garzaya da shi asibiti
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: INEC za ta haramtawa masu kad'a kuri'a amfani da wayoyi a rumfunan zabe

"Babu wani abun damuwa akan rashin lafiyar sa, domin kuwa zuwa ranar Lahadi za'a sallame shi. Yana bukatar hutu ne, abubuwan sun yi masa yawa," a cewar makusancin.

Har zuwa hada wannan rahoton babu wani tabbacin na lalurar da ke damun shugaban, sai dai wani makusancin sa ya ce hakan ba zai rasa nasaba da tsufa ba.

A ranar 13 ga watan satumba Sanata ladoja ya jagoranci mambobin jam'iyyar sa zuwa ga Ile Ife a jihar Osun don kaddamar da yakin zaben dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar, a shirin fuskantar zaben jihar na mako kai zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel