Sarkin Ogoni ya nada wa Shugaba Buhari sarauta

Sarkin Ogoni ya nada wa Shugaba Buhari sarauta

Wani sarkin Ogoni, G.N.K. Ogininwa ya nada wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, sarauta a ranar Juma’a, 14 ga watan Satumba.

Sunan sarautar da aka nada wa shugaban kasar “Meni-Doo-Lenu” wato ma’ana sarkin abubuwan alkhairi na kasar Ogoni.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman a kafofin watsa labarai, Femi Adesina yace an ba shugaban kasar wannan sarauta ne lokacin da ya karbi bakuncin tawagar shugabannin Ogoni daga masarautar Ogoni, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Sarkin Ogoni ya nada wa Shugaba Buhari sarauta
Sarkin Ogoni ya nada wa Shugaba Buhari sarauta
Asali: Facebook

Ogoni-Land ya kasance daya daga cikin manyan yakunan dake samar da man fetur a Najeriya. An san yankin da matsaloli da dama musamman akan mai.

KU KARANTA KUMA: Rikicin shugabancin ya kaure tsakanin bangarori biyu na APC a jihar Arewa

A yayin ziyarar, shuwagabannin sun bukaci Buhari ya karrama marigayi Ken Saro-Wiwa, haka zalika sun bashi dama ya gabatar masu da gwamnan jihar Rivers na gaba.

Daga cikin tawagar akwai Gbenemene na masarautar Tai, wakilan addinai na MOSOP, KAGOTE, da kuma mambobin majalisar sarakunan gargajiya na yankin Ogoni.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel