Yanzu yanzu: An yi awon gaba da mata masu yawa a sabon harin Adamawa

Yanzu yanzu: An yi awon gaba da mata masu yawa a sabon harin Adamawa

- Wasu mutane da ake zargin makiyaya ne sun yi awon gaba da mata a wani hari da suka kai kauyukan karamar hukumar Numan da ke jihar Adamawa

- Hon. Tayedi, yar majalisar da ke wakiltar Numan, ta yi ikirarin cewa maharan sun fito ne daga yankin Abbare, inda ke da tarin sojoji a wajen

Wasu mutane da ake zargin makiyaya ne sun yi awon gaba da mata a wani hari da suka kai kauyukan Gwon, Bolki da Nzumosu a karamar hukumar Numan da ke jihar Adamawa.

Garuruwan da ke cikin karamar hukumar Numan na ci gaba da fuskantar hare hare tun daga farkon watan Janairun wannan shekarar, hare haren da hukumomi ke kallon ya zarce a kirashi da rikicin makiyaya da manoma.

Da ta ke tabbatar da faruwar harin, yar majalisa mai wakiltar mazabar Numan a majalisar dokoki ta jihar, Mrs. Sodom Tayedi ta shaidawa manema labarai cewa makiyayan na ci gaba da mamaye sauran garuruwan da ke makwaftaka da su.

KARANTA WANNAN: Duk kanwar ja ce: Idan har PDP barayi ne to APC ma barayi ne - Lamido

Yanzu yanzu: An yi awon gaba da mata masu yawa a sabon harin Adamawa
Yanzu yanzu: An yi awon gaba da mata masu yawa a sabon harin Adamawa
Asali: Facebook

Ta bayyana cewa zuwa yanzu ba'a san adadin mutanen da lamarin ya shafa ba, sakamakon mutane sun gudu don buya a cikin dazuzzuka.

Hon. Tayedi, ta yi ikirarin cewa maharan sun fito ne daga yankin Abbare, inda ke da tarin sojoji a wajen.

"Akwai sojoji a Abbare, amma hakan bai hana maharan fitowa daga yankin ba" a cewar ta.

Ta ci gaba da cewa: "Babu wani lokaci da suka kawo hari, ni kuma ban kira jami'an tsaro ba a matsayina na wakiliyarsu. Yanzun nan na kira kwamandan wata runduna, ya tabbatar min dakarun soji na zuwa yanzu"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel