Boko Haram: Gaskiyar abun da ya auku a kauyukan Damsak da Gudumbali a jihar Borno
- Gaskiyar abun da ya auku a kauyukan Damsak da Gudumbali a jihar Borno
- An ce bangaren Al-Barnawi ne suka kai harin
- Sojoji suka kai wa hari ba 'yan gari ba
Labarin da muka samu daga majiyoyin mu game da ainihin abun da ya faru a kauyukan Damsak da Gudumbali shine cewar bangaren Al-Barnawi ne suka kai harin a garuruwan da ake magana a jihar Borno ta yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Yan kasuwa sun kunyata El-rufai a Kaduna
Harin dai ance bangaren 'yan Boko Haram din ne na Al Barnawi dake da goyon bayan 'yan ta'addan ISIS na duniya watau Islamic State in West Africa a turance (ISWA).
Legit.ng hakazalika ta samu cewa 'yan ta'addan sun shiga kauyukan ne da muggan makamai daban-daban amma sai dai kuma basu nemi farar hula ba sai dai sojojin dake wurin kawai.
A wani labarin kuma, Bangaren masana tattalin arzikin kasa watau Economist Intelligence Unit (EIU) na wata mujallar birnin Landan watau The Economist Magazine ta yi hasashen faduwar Shugaba Buhari zaben 2019 da za'a gudanar.
Mujallar dai wadda ake bugawa a birnin na Landan haka zalika tayi hasashen cewa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ce zata lashe zaben da za'a gudanar nan da 'yan watanni kadan.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng