Dara ta ci gida: An cafke marubuciyar littafin 'Yadda zaki kashe mijinki' da laifin kashe mijinta

Dara ta ci gida: An cafke marubuciyar littafin 'Yadda zaki kashe mijinki' da laifin kashe mijinta

Nnancy Crampton-Brophy wacce ta taba rubuta wani littafi mai suna 'Yadda zai kashe mijinki', ta shiga hannun hukuma bisa zargin kashe mijinta

A 2012, Cramptom-Brophy ta shaidawa shafin yanar gizo na Genres dalilan da ke bata sha'awar rubuta litattafan soyayya na kisan kai ko tashin hankali

Mijin nata mai shekaru 63, ya gamu da ajalinsa bayan da aka harbe shi har lahira a wani dakin dafa abinci a jami'ar Oreon Culinary, a ranar 2 ga watan Yuni

Wata marubuciyar littattafan soyayya na tashin hankali, Nnancy Crampton-Brophy, mai shekaru 68, wacce ta taba rubuta wani littafi mai suna 'Yadda zai kashe mijinki', ta shiga hannun hukuma bisa zargin kashe mijinta mai suna Dan Brophy.

Rundunar yan sanda a Portland, Oregon, US sun cafke Crampton-Brophy a ranar Larabar da ta gabata tare da gurfanar da ita a gaban kotu bisa aikata laifin kisan kai da kuma amfani da makamin da aka haramtawa jama'a amfani da shi.

Mijin nata mai shekaru 63, wanda shima ya taba yin aikin yan sanda, ya gamu da ajalinsa bayan da aka harbe shi har lahira a wani dakin dafa abinci a jami'ar Oreon Culinary, a ranar 2 ga watan Yuni, wanda a farko aka gaza gane wanda yayi kisan.

KARANTA WANNAN: Buhari ya bukaci yan Nigeria su zabi APC don gujewa kuskuren 1999 zuwa 2015

Dara ta ci gida: An cafke marubuciyar littafin 'Yadda zaki kashe mijinki' da laifin kashe mijinta
Dara ta ci gida: An cafke marubuciyar littafin 'Yadda zaki kashe mijinki' da laifin kashe mijinta
Asali: Getty Images

Sai dai an gurfanar da Crampton-Brophy a gaban kotu da aikata laifin kisa, inda yan sanda da masu shigar da kara suka ja bakinsu sukayi gum akan lamarin.

A ranar da aka yi kisan, marubuciyar litattafan 'Mijin da bai dace ba' da kuma 'Abubuwan da yan mata za su iya aikatawa', ta shiga shafinta na Facebook, inda ta bayyana kaduwa da kin amincewa da mutuwar mijin nata.

A 2012, Cramptom-Brophy ta shaidawa shafin yanar gizo na Genres dalilan da suke bata sha'awar rubuta labaran soyayya masu alaka da kashe kashe ko tashin hankali.

"Tunani na labaran kisan kai, tashin hankali da zubar da jini, na ziyartar zuciya da kwakwalwata a kowane lokaci, wanda a tunani na hakan ne ya sa mijina ya koyi kwanciya barci da ido daya" a zantawarsa da shafin yanar gizo na Genres.

A cewar takardartuhumar da aka gabatar gabatan kotu, miji da matar sun kasance ma'aurata na tsawon shekaru 27.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel