Yan takaran kujerar kujeran shugaban kasa a PDP sun shirya nemawa kansu mafita kafin zaben fidda gwani

Yan takaran kujerar kujeran shugaban kasa a PDP sun shirya nemawa kansu mafita kafin zaben fidda gwani

- Yan takaran kujerar kujeran shugaban kasa a PDP sun shirya nemawa kansu mafita kafin zaben fidda gwani

- Wadannan yan takara sun hada da Bukola Saraki, David Mark, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Sanata Jonah Jang, Gwamna Tambuwal da Ibrahim Dankwambo

- Sun yanki fam dinsu ne ta hanyar da zai basu damar takarar wani matsayin idan basu samu tikitin takaran shugaban kasa ba

Wasu yan takarar kujeran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na shirin samarwa kansu mafita koda su gaza samun tikitin jam’iyyar a zaben fidda gwani na jam’iyyar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, David Mark, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Sanata Jonah Jang duk suna neman tikitin jam’iyyar PDP.

Yan takaran kujerar kujeran shugaban kasa a PDP sun shirya nemawa kansu mafita kafin zaben fidda gwani
Yan takaran kujerar kujeran shugaban kasa a PDP sun shirya nemawa kansu mafita kafin zaben fidda gwani
Asali: Original

Amma dukkaninsu sun nemi takara ne ta hanyar da zai basu damar dawowa majalisar dattawa idan basu cimma kudirinsu na tsayawa takarar shugabna kasa ba.

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da Ibrahim Dankwambo na jihar Gombe, wadanda suma neman takarar kujerar shugaban kasa suke yi, ba’a bar su a baya ba yayinda tsohon kakakin majalisar wakilai ke kokarin ganin ya rike kujerarsa na gwamna a matsayin mafita, Dankwambo kuma na neman komawa majalisar dattawa a matsayin mafita.

KU KARANTA KUMA: Buhari bai samu abokin adawa ba, zai fuskanci zaben fidda gwani na APC a Oktoba don tabbatar da shi

Jam’iyyar PDP ta sanya ranar 30 ga watan Satumba ranar zaben fidda gwani na majalisar dattawa da wakilai sannan na kujerar shugaban kasa zai zo a ranakun 5 da 6 ga watan Oktoba.

Farashin fam din takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar naira miliyaan 12, yayinda na kujerar majalisar dattawa ya kama naira miliyan hudu sannan na kujerar gwamna ya kama naira miliyan shida.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel