Amina Muhammad ta bayyana dalilin da yasa ake kiran ministar shara a Nigeria
- Amina Mohammed, mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya MDD, ta bayyana dalilin da ya sa ake kiranta ministar shara a Nigeria
- Mohammed ta ce da yawan mutane ba su san daraja da girman ofishinta na ministar muhalli ba
- Tsohuwar ministar, wacce uwa ce ga 'yaya shida, ta yi jawabi kan wasu kudurori 17 da suka gina hukumar dorewar cimma muradun karni SDGs
Amina Mohammed, mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya MDD, ta bayyana dalilin da ya sa ake kiranta ministar shara a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nadata a matsayin ministar muhalli.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Mohammed ta bayyana hakan a ranar Talata, 11 ga watan Satumba, inda ta ce mutane na kiranta da sunan ne saboda rashin sanin daraja da muhimmancin ofishinta na ministar muhalli ba.
Legit.ng ta tattara rahotanni da suke nuni da cewa ta bayyanana hakan a lokacin wata tattaunawa tsakanin MDD da hukumar IMF, don samar da hanyoyin karfafa ayyukan raya kasashe.
KARANTA WANNAN: Ambaliya ta kashe mutane 10 tare da lalata daruruwan gidaje a Adamawa - SEMA

Asali: Depositphotos
Ta yi murabus daga majalisar zartaswa ta kasa a ranar 24 ga watan Febreru 2017, inda ta fara sabon aikinta a matsayin mataimakiyar babban sakataren majalisar dinkin duniya.
A cewar ta: "Bari in baku wani labari, a lokacin da na koma Nigeria a matsayin minista, yan jihata na tambayata wai dama ma'aikatar muhalli aka bani? domin wannan aikin kwashewa da zubar da shara ne, ke nan na zama macen bola. Sun kasa gane cewa muhalli ya fi karfin zubar da shara kadai."
Ta ce akwai bukatar majalisar dinkin duniya da hukumar IMF su tattauna akan muhimman inganta samar da hanyoyin bunkasa tattalin arziki, da kuma nemo hanyoyin bunkasa rayuwar al'umma.
Tsohuwar ministar, wacce uwa ce ga 'yaya shida, ta yi jawabi kan wasu kudurori 17 da suka gina hukumar dorewar cimma muradun karni SDGs, ta ce gaba daya kudurorin na da muhimmanci ga makomar duniya baki daya
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng