Ambaliya ta kashe mutane 10 tare da lalata daruruwan gidaje a Adamawa - SEMA

Ambaliya ta kashe mutane 10 tare da lalata daruruwan gidaje a Adamawa - SEMA

- Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Adamawa ADSEMA, ta ce mutane goma ne ambaliyar ruwa ta yi silar ajalisu yayin da daruruwa suka rasa gidaje

- Babban sakataren hukumar, Dr. Muhammad Suleiman ya ce ambaliyar ta yi sanadi mutuwar daruruwan dabbobi da tsuntsaye na gida

- Rahotanni sun bayyana cewa akalla jihohi 12 ne ambaliyar ruwa ta shafa a wannan shekarar

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Adamawa ADSEMA, ta ce akalla mutane goma ne ambaliyar ruwa tai silar ajalisun yayin da daruruwan mutane suka rasa gidajensu, bayan da aka tafka wani ruwa kamar da bakin kwarya a jihar.

Babban sakataren hukumar, Dr. Muhammad Suleiman ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a ranar Alhamis dinnan a garin Yola.

Suleiman ya ce ambaliyar ta yi sanadi mutuwar daruruwan dabbobi da tsuntsaye na gida.

KARANTA WANNAN: Nigeria ta fi kowace kasa a Afrika bunkasar tattalin arziki - Rahoton Forbes

Ya ce an samu asarar rayukan mutanen ne a kananan hukumomin kudancin Yola, Guyuk, Lamurde da kuma Song.

Ambaliya ta kashe mutane 10 tare da lalata daruruwan gidaje a Adamawa - SEMA
Ambaliya ta kashe mutane 10 tare da lalata daruruwan gidaje a Adamawa - SEMA
Asali: Twitter

"Ambaliyar ruwa na so ta zama babbar barazana garemu a nan Adamawa, domin kuwa waki'ar na daga hankulan jama'a. Mun rasa mutane 10, yayin da daruruwan mutane suka rasa gidajensu, haka zalika an rasa dabbobi da tsuntsayen gida.

"Haka zalika,ambaliyar ruwan ta shanye gonakin mutane a cikin kananan hukumomi 9 da ke makwaftaka da tekun Benue, wanda hakan yayi sanadin lalata amfanin gonar jama'a" a cewar Suleiman.

Suleiman ya ce sama da rabin adadin mutanen jihar ke fuskantar wannan barazanar ta ambaliyar ruwa, tare da yin kira ga daukacin al'ummar jihar da su kasance masu shirin ko ta kwana.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito cewa akalla jihohi 12 ne ambaliyar ruwa ta shafa a wannan shekarar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel