Masarautar Kano na shirin fitar da doka akan yawaitar mutuwar aure
Masarautar Kano ta dukufa wajrn aiki akan wani kudirin doka da zai kawo karshen matsalar yawan mutuwar aure tare da tursasa wa magidanta daukar cikakkiyar dawainiyar iyalansu.
Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi na II ya bayyana hakan a lokacin zantawa da manema labarai a bayan wani taro da Asusun Tallafawa al’umma na Majalisar Dinkin Duniya ya shirya a babban birnin tarayya, Abuja.
Sarkin wanda ya samu wakilcin Talban Kan, ya ce Masarautar ba za ta yarje wa maza sakin matansu ba tare da daukar hidindimun kulawa da yaransu ba.

Asali: Facebook
Ba da dadewa ba kwamitin da ke aiki kan dokar zai kammala aikinsa kafin gabatar da shi ga Majalisar Dokokin Jihar domin amincewa da shi a matsayin doka.
KU KARANTA KUMA: APC tayi magana akan sauya shekar da Dogara yayi zuwa PDP
Kwamitin ya kunshi manyan alkalai da malaman addinin musulunci da na zamani.
Ana sanya ran dokar za ta taka gagarumar rawar gani wurin rage raragaitar kananan yara a kan titunan jihar matukar gwamnati ta amice da ita.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng