Anyi musayar wuta tsakanin yan Boko Haram da Soji a Damasak

Anyi musayar wuta tsakanin yan Boko Haram da Soji a Damasak

Labarin da ke shigo mana yanzu na nuna cewa ana artabu tsakanin rundunar 145 Birgade da yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram a garin Damasak, jihar Borno.

Jami'an sojin sun shiga musayar wutan ne yayinda ya Boko Haram suka kawo musu hari a inda suke zaune misalin karfe 6 na yamma. Tun lokacin ana ruwa harsasai.

Legit.ng ta samu wannan rahoto ne daga kakakin hukumar sojin Najeriya, Birgediya Janar Texas Chukwu.

Daga baya, hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewa an samu nasarar kashe dimbin yan Boko Haram a wannan artabu da ya faru a Damasak. Kana ta kara da cewa yaki da yan ta'adda na cigaba da samun nasara a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

KU KARANTA: Yakubu Dogara ya siya Fam na PDP ba tare da ya bar APC ba

Hukumar ta karyata rahoton Sahara Reporters cewa yan Boko Haram sun fitittiki Sojoji kuma sun kwace garin Damasak. Ta yi kira ga kafafen yada labarai da su guji yada jita-jitan karya ga al'umman Najeriya.

A karshe, hukumar ta shawarci mazauna yankin da su fita harkokinsu na ya da kullum saboda hukumar na tabbatar musu da cewa za ta kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Kwanakin bayan nan yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun dau sbaon salon kaiwa jami'an soji hari a barikinsu sabanin kunar bakin wake da suke tura yara. Wannan ya haddasa hallakan rayukan sojoji da dama musamman a Gudumbali.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel