2019: Okorocha ya sallami kwamishinoni 13 da hadimai

2019: Okorocha ya sallami kwamishinoni 13 da hadimai

- Gwamna Rochas Okorocha ya sallami wasu kwamishinoni da hadimansa

- Wadanda aka sallama dai na neman takara ne a karkashin jam'iyyar APC

- An sallame su ne domin su samu damar fuskantar harkokin siyasarsu kafin zaben fidda gwani

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo a ranar Laraba, 12 ga watan Satumba ya sallami sakataren gwamnatin jihar, George Eche, shugaban ma’aikatansa, Uche Nwosu, mataimakin shugaban ma’aikata, Kingsley Uju da babban sakatarensa, Paschal Obi.

Sauran da lamarin ya shafa sune, Emma Ojinero, kwamishinan kasuwanci, Farfesa Nnamdi Obiaraeri, kwamishinan bayanai, Ngozi Njoku, kwamishinan ci gaban jama’a.

2019: Okorocha ya sallami kwamishinoni 13 da hadimai
2019: Okorocha ya sallami kwamishinoni 13 da hadimai
Asali: Depositphotos

Joy Mbawuike, kwamishinan ci gaban kasuwanci, Obinna Mbata, kwamishinan kudi, Dan Nworie, kwamishinan ilimi, Simeon Iwunze, mai bada shawara na musamman akan sabonta birane, Obinna Amagwula, mai ba da shawara na mussaman akan ayyuka na baki daya da kuma Betty Uzoma, hadima na musamman ka kudi.

KU KARANTA KUMA: Buratai ya mayar da hedkwatar rundunar sojoji zuwa Gudumbali

A wata sanarwa daga babban sakataren labarai na gwamnan, Sam Onwuemeodo, a Owerri ya bayyana cewa wadanda abun ya shafa na neman takara ne a jam’iyyar the All Progressives Congress (APC).

An sallame su ne domin samun damar mayar da hankali ga takaransu gabannin zaben fidda gwani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel