Tazarcen Buhari zai tabbatar da dama ga matasa – Shugabar matan APC

Tazarcen Buhari zai tabbatar da dama ga matasa – Shugabar matan APC

- Shugabar matan APC ta bukaci matasa da su Shugaba Buhari goyon bayansu a 2019

- Hajia Salamatu tace tazarcen Shugaban kasar zai samawa matasa damar da za'a dama dasu a gwamnatin tarayya

- Ta kuma jadadda cewa Buhari zai daukaka martabar kasar a tsakanin takwarorinta na duniya

Shugabar mata na jam’iyyar All Progressive Congress (APC) na kasa, Hajia Salamatu Bawa, tace tazarcen Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019 shine hanya mafi inganci da za’a samu ci gaba da kuma dama ga matasa a matsayin masu ruwa da tsaki a gwamnatin tarayya.

Tayi magan ne yayinda matasa suka je yi mata ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarta a Ayamgba, jihar Kogi.

Hajiya Bawa tace: “Buhari mutun ne mai kwari, mutunci kuma masoyin mulkin damokradiya. Zai taimaka wajen inganta kasar da zai hau da Najeriya tudun tsira sannan zzai kare martabar kasar ya kuma daukakata a tsakanin kasashen duniya."

Tazarcen Buhari zai tabbatar da dama ga matasa – Shugabar matan APC
Tazarcen Buhari zai tabbatar da dama ga matasa – Shugabar matan APC
Asali: Depositphotos

Ta kara da cewa tazarcen Buhari zai ba matasa damar cimma burinsu da koyon ayyuka da mafarkinsu su zamo gaskiya, sannan kuma su zama ana yi dasu wajen kawoci gaban siyasa da tattalin arziki kasar ta hanyar bayar da nasu gudunmawar sannan kuma cewa zai samar da ayyukan yi da dama ta hanyar bunkasa harkar noma da sauran hukumomin kasar, kasuwanci da kasuwannin da zai tabbatar da sana’o’in hannu.

KU KARANTA KUMA: Bani da matsala da Gwamna Abubakar - Oshiomhole

A nashi bankalen, shugaban kwamitin kare damokradiyya, Dr. Pat Anyanwu ya bukaxi matasa da tashi don kare damokradiyya, cewa su bayar da kaso 80 na kuri’unsu ga Shugaba Buhari wanda ya amince da dokar ba matasa damar da za’a dama dasu a harkar siyasa wato, Not-Too-Young-to-Run.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel