An tsare jigon APC kan zargin sukar gwamnan Bayelsa

An tsare jigon APC kan zargin sukar gwamnan Bayelsa

Kwamitin abokai na wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) babin jihar Rivers, Perekeme Kpodoh, sun nemi dauki akan ci gaba da tsare shi da ake yi wadda a cewarsu akwai siyasa cikin lamarin.

Kwamitin karkashin jagorancin shugabanta, George Fubara, da sakatarenta Chidi Uchena sunyi gargadin cewa za’a tunzura su fallasa wasu lamura da dama dake boye idan har ba’a saki Kpodoh wani jigon APC a Bayelsa ba.

A cewarsu a yanzu aka hana horar da Kpodoh saboda ya yi Magana akan gwamnatin Gwamna Seriake Dickson.

Sunce gwamnan ya fusata ne bayan Kpodoh ya rubuta wani jawabi inda ya bukaci gwamnan da ya daina tafiye-tafiye marasa amfani ya fuskanci gwamnatinsa.

An tsare jigon APC kan zargin sukar gwamnan Bayelsa
An tsare jigon APC kan zargin sukar gwamnan Bayelsa
Asali: Depositphotos

“Gwamnan ya sake tunzura bayan Kpodoh ya bukace shi da ya mayar da martani da zargin da tsohon gwamnan jihar, Timipre Sylva ke yi masa kan yadda gwamnatinsa tayi da bashin dake makale a wuyarta”, kungiyar ta fadi hakan yayin da tayi ikirarin cewa an tsare jigon na APC din ne akan wani zargin fyade wadda aka dade da watsarwa.

Kungiyar sun ce matar da ake Magana akai na kara akan hannu akan sace kudi N500,000.

KU KARANTA KUMA: 2019: Nine gaba da Atiku, ba zan janye masa ba - Lamido

A cewarsu an shigar da kara wani ofishin yan sanda. Sai dai matar ta sake ikirarin cewa an yi mata fyade a wani ofishin yan sanda daban kuma.

An tattaro cewa anyi watsi da lamarin bayan an gano gaskiya.

Don haka sun bukaci a kawo masa agaji domin a cewarsu rayuwarsa na cikin barazana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel