WhatsApp ya ja an yi ram wasu Bayin Allah a Kano

WhatsApp ya ja an yi ram wasu Bayin Allah a Kano

Sakamakon yada labaran karya game da wata matar aure da aka ce tana safaran kananan yara, yan sanda a jihar Kano sun kama shugaba da mambobin wani kungiyar sadarwa ta Whatsapp.

Magaji Musa Maaji, kakakin rundunar yan sandan Kano, ya bayyana cewa an kama masu laifin ne bayan wata mata ta kai korafi hukumar yan sandan.

A cewar Magaji: “Mun samu korafi daga wata matar aure da wani ma’aikacin gwamnati, Misis Bushirat Madakim, cewa ana yada hoton ta a wani shafin WhatsApp inda ake yi mata kazafi.

WhatsApp ya ja an yi ram wasu Bayin Allah a Kano
WhatsApp ya ja an yi ram wasu Bayin Allah a Kano
Asali: Twitter

"Da muka ji korafinta, kwamishinan yan sandan, Alhaji Rabiu Yusuf, ya bukaci ayi binciken gaggawa, inda ana suka bi har suka kama mutane uku masu aure, namiji guda da mata biyu, kan laifin yada bayanan karya.

“Da aka tunkare su akan tuhumar da ake yi masu, masu laifin sun yarda cewa hoton matar a shafinsu.

KU KARANTA KUMA: 2019: Dasuki ya shiga tseren takarar gwamna a Gombe

“Sun jadadda cewa basu taba ganin matar ko zantawa da ita ba kafin su fara yada labarin, inda suka bukaci a yafe masu."

A yanzu dai an bayar da belin mutanen yayinda ake ci gaba da bincike akan lamarin. Sannan yan sanda na ba matar kariya saboda hotonta da yayi yawo da gudun kada fusatattu su far mata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel