2019: Ba zamu hakura cikin sauki kamar Jonathan ba – Magoya bayan Atiku

2019: Ba zamu hakura cikin sauki kamar Jonathan ba – Magoya bayan Atiku

- Jam'iyyar PDP ta kaddamar da cewa ba zata mika mulki ga APC cikin sauki kamar yadda Jonathan yayi a 2015 ba

- Sanata Abdul Ningi yace ba zasu nade hannu su ga faduwarsu ba

- Ya kuma bukaci magoya bayan Atiku da Lamido da su hada kansu wajen marawa duk wadda yayi nasara baya

Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), ta kaddamar da cewa ba zata mika mulki ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kamar yadda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi a 2015 ba.

Sanata Abdul Ningi wadda ya mikewa Otunba Gbenga Daniel, Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 10 ga watan Satumba a lokacin ziyarar kamfen din mataimakain shugaban kasa Atiku Abubakar a Dutse, jihar Jigawa.

2019: Ba zamu hakura cikin sauki kamar Jonathan ba – Magoya bayan Atiku
2019: Ba zamu hakura cikin sauki kamar Jonathan ba – Magoya bayan Atiku
Asali: UGC

Sanata Ninge yace: “A 2019 ba zai yi sauki ga APC idan tana sa ran ganin karamci da tsohon shugaban kasarmu yayi wa Buhari duk da cewar ba’a kammala fadin sakamako ba.

“Jonathan mutun ne mai saukin kai da ya amshi kaye tun ma kan a kammala zabe, har fatan alkhairi da murna muka taya APC akan nasarar da tayi amma a wannan lokacin ina ba ku tabbacin ba zamu nade hannuwanmu muji labarin rashin nasaranmu ba.”

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi jaje ga gwamnati da mutanen jihar Nasarawa kan fashewar gas

Ningi wanda ya kasance dan takaran gwamna daga jihar Bauchi, yace Atiku Abubakar da Sule Lamido sun yi nisa a harkar siyasarsu da kuma dangantakarsu, inda ya shawarci magoya bayansu da kada su shagala, amma su marawa kowanne daga cikinsu da ya samu tikitin wakiltan jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel