Gwamnan jihar Rivers ya zargi shugaba Buhari da kitsa tuggun kawar dashi daga duniya

Gwamnan jihar Rivers ya zargi shugaba Buhari da kitsa tuggun kawar dashi daga duniya

- Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya zargi gwamnatin shugaba Buhari karkashin APC da kitsa makircin kashe shi don kwace jihar Rivers da karfin tsiya

- Sai dai, fadar shugaban kasa ta karyata wannan zargi na Wike, tana mai cewa shugaba Buhari bai taba sa hannu a harkokin ta'addanci

Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike, a cikin wata zantawa da yayi da manema labarai, ya ce: "Na sanar da matata da yarana, dangane da wannan mugun kullun na gani bayana da suke son yi. Irin rayuwar da muka tsinci kawunan mu a ciki kenan, ace gwamnati kamar tana jin kishin shan jani.

"Na sanar da su cewa in dai a bakin aikina ne, to sai dai in rasa rayuwata. Dole ne mu mike mu kare gaskiya tare da yakar karya. Dukkan alamomi sun bayyana karara, gwamnati ta shirya wannan makirci, mu kuma a shirye muke mu mutu.

"Suna iko akan komai da kowa, zasu iya turo rundunar soji sun maishe da gari kufai. Wannan gwamnati ce da bata shakkar aiwatar da mugun nufinta, wannan ba gwamnatin demokaradiya bace, gwamnatin kama karya ce. Bani da masaniya ko zan dade a raye, amma zasu iya kashe ni idan lokaci na bai yi ba?

"Tabbas mutuwa zata zo, amma sai lokaci ya yi, dole ne mu tashi mu fuskanci gaskiya. Ba zan manta ba, Antoni Janar dina ya zo don gani na, na sanar da shi cewa dole ya bar kasar, koda don ya je duba lafiyarsa ne, amma daga karshe dai saida ya mutu, ban sake ganinsa ba.

KARANTA WANNAN: Rikici ya kunno kai a Jam'iyyar PDP sakamakon wani sabon hukunci da ta yanke

Gwamnan jihar Rivers ya zargi shugaba Buhari da kitsa tuggun kawar dashi daga duniya
Gwamnan jihar Rivers ya zargi shugaba Buhari da kitsa tuggun kawar dashi daga duniya
Asali: Depositphotos

"Koda kana a cikin gidanka ne, gwamnati zata zo ta same ka, ko da kana a kicin, gwamnati zata zo ta riske ka, kai koda kana a cikin ofishinka ne, gwamnati zata iya bibiyarka.

"Ba wai zance bane na jin tsoro, ya dai zama wajibi ne mu fadawa kawunanmu gaskiya. Wannan gwamnatin ta shirya kawar da duk wanda ya ce mata "A'a". Wannan ne ma nace kasashen waje ba sa yin abubuwan da ya dace, zuwa yanzu ya kamata su dakatar da aikin takardu fita kasashen waje na wasu yan Nigeria, don basa bin dokokin demokaradiya.

"Bari na sanar da ku wannan, suna kokarin karawa kwamishinan yan sanda na jihata matsayi zuwa mataimakin sifeta janar, suna kokarin karawa mataimakin kwamishinan matsayi don ya koma kwamishina. Kuma suna kitsa wannan kawai saboda zaben 2019, shin ko suna tunanin bamu sani ba?"

Sai dai da ya ke maida martani, wata majiya daga cikin fadar shugaba kasa, ya ce wannan kalami na Wike abun ayi dariya ne, saboda wanda ake zargi da yin sanadin zubar da jini, bai isa ya zargi shugaba Buhari da harin rayuwarsa ba.

Majiyar ta shaida cewa, fadar shugaban kasa na shirin saka kafar wando daya da gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti da kuma gwamna Wike, yana mai cewa shugaban kasa na matukar takaicin yawan barkewar ta'addanci a jihar Rivers.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel