Digiri na 3 da Gwamna Ortom ya mallaka na jabu ne – Akume

Digiri na 3 da Gwamna Ortom ya mallaka na jabu ne – Akume

- Sanata George Akume da Gwamna Samuel Ortom sun yi musayar zafafan kalamai

-Akume yace digiri na uku da gwamnan ya mallaka na jabu ne

- Ya kalubalanci Ortom da ya biya ma'aikata da yan fansh bashin alashi da suke bin sa

- Kakakin gwamnan kuma ya bayyana Akume a matsayin mashayi da bai kamata a karbi zancensa ba

Sanata mai wakiltan mazabar arewa maso gabashin Benue, George Akume da Gwamna Samuel Ortom sun yi musayar zafafan kalamai a ranar Litinin, 10 ga watan Satumba.

Akume a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka gudanar a dakin taron Castle Event Centre, Makurdi a ranar Lahadi, 9 ga watan Satumba ya bayyana Ortom a matsayin mara kokari, tare da zargin cewa gwamnan na dauke da digiri na uku na jabu.

Digiri na 3 da Gwamna Ortom ya mallaka na jabu ne – Akume
Digiri na 3 da Gwamna Ortom ya mallaka na jabu ne – Akume
Asali: Depositphotos

Akume wadda ya zargi gwamnan da tafiyar da shirin zuba jari a al’umma kamar gadon gdansu ya bayyana cewa akwai bukatar a yi waje dashi daga kan kujerar mulki a shekara mai zuwa.

Akume ya kuma zargi Ortom da yawan zagin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Rikici ya kunno kai a Jam'iyyar PDP sakamakon wani sabon hukunci da ta yanke

Ya kalubalanci gwamnan da ya biya bashin albashin ma’aikata da nay an fansho da suke bin shi a jihar wadda a cewarsa yunwa na hallaka su.

Amma da yake mayar da martani a madadin ubangidansa, kakakin Ortom, Taav Agerzua ya bayyana Akume a matsayin mashayin da bai kamata a dauki maganarsa da ma’ana ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel