Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta kama hanyar fitar da dan takara daya da zai kara da Buhari

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta kama hanyar fitar da dan takara daya da zai kara da Buhari

- Jam'iyyar PDP ta kama hanyar fitar da dan takara daya a zaben 2019

- Shugaban kwamitin amintattun, Sanata Walid Jibrin shine ya sanar da hakan

- Akwai akalla mutane 12 da ke neman tikitin jam'iyyar

Babban kwamitin amintattu na jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP), ya ce tuni yayi nisa wajen ganin ya kwantar da dukkan wata fitina da ka iya tasowa zaben fitar da gwanin dan takarar jam'iyyar na shugaban kasa a ranar 6 ga watan Okotoba mai zuwa.

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta kama hanyar fitar da dan takara daya da zai kara da Buhari
Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta kama hanyar fitar da dan takara daya da zai kara da Buhari
Asali: UGC

KU KARANTA: Na hannun daman Jonathan na neman jefa shi cakwakiya

Shugaban kwamitin amintattun, Sanata Walid Jibrin shine ya sanar da hakan a garin Abuja, ranar Litinin din da ta gabata inda ya bayyana cewa kawo yanzu dai suna ta kokarin ganin 'yan takarar dukkan su sun amince da sasancin da zai fito da mutum daya a tsakanin su.

Legit.ng dai ta samu cewa jam'iyyar ta Peoples Democratic Party (PDP) yanzu haka tana da jumlar jama'a sha biyu da suka nuna sha'awar su ta tsayawa takarar shugaban kasa a inuwar ta da kuma suka sayi fom din takarar.

Idan dai ba'a manta ba manya daga cikin masu neman takarar karawa da shugaba Buhari da ke zaman dan takarar jam'iyyar APC daya tilo sun hada da Atiku Abubakar, Sanata Kwankwaso, Sule Lamido, Gwamna Dankwambo da Tambuwal da dai sauran su.

A wani labarin kuma, Kamfanin sadarwar nan na MTN a Najeriya ya maka babban bankin na Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN), da kuma Antoni Janar na kasar kuma ministan shari'a a gwamnatin shugaba Buhari kotu yana neman a bi masa hakkin sa.

Kamar dai yadda muka samu, shi dai kamfanin a ranar Litinin din da ta gabata ne ya shigar da karar kotu a garin Abuja, yana kalubalantar matakin da gwamnatin Najeriya ta kakaba masa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel