Harin Borno: Wadanda suka tsira daga Boko Haram sun bayyana halin da suka shiga

Harin Borno: Wadanda suka tsira daga Boko Haram sun bayyana halin da suka shiga

Wadanda suka tsira daga harin da yan ta’addan Boko Haram suka kai yankin Gudumbale, karamar hukumar Guzamala dake jihar Borno, a ranar Asabar 8 ga watan Satumba sun bayyana halin tsaka mai wuya da suka shiga a lokacin lamarin.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa yan ta’adda da dama daauke da makamai sun mamaye garin sannan suka kai hari ga sansanin sojoji, fadan day a kwashe kimanin sa’o’i 12.

Wasu da suka tsira daga harin sun zanta da NAN bayan sunyi nasarar tserewa Maiduguri a yammacin ranar Lahadi, 9 ga watan Satumba inda suka bayyana ra’ayoyinsu akan lamarin.

Hajja Bintu Bukar, uwar yara uku mai shekaru 33 tace yan ta’addan sunyi tsare su na tsawon sa’o’i da dama sannan suka ci gaba da harbe-harbe na tsawon lokacin.

Harin Borno: Wadanda suka tsira daga Boko Haram sun bayyana halin da suka shiga
Harin Borno: Wadanda suka tsira daga Boko Haram sun bayyana halin da suka shiga
Asali: Facebook

“Bazan iya bayyana irin jimamin da na shigaba ba. Ina ta jiran su faso gidanmu su kashe mu. Suna ta ihun Allahu Akhbar a yayinda suke harbe-harbe daga kusa da inda muke.

“Dukkaninmu mun kwanta a kasa saboda tsoron kada harbi ya same mu. Sun cigaba da harbe-harbe har karfe 3 na tsakar dare.

"Lokacin ne muka tsere muka fara gudu. Na rike hannayen yarana uku sosai saboda gari bai waye ba akwai tsananin duhu. Na kuma gano wasu yara biyar mallakar makwabtana da suka tsere sai na rike su sosai.

“Mun taka sama da kilomita 20 inda wasu motoi dauke da yan gudun hijira suka taimake mu zuwa Gajiram. Daga nan ne muka zo Maiduguri.

“Har yanzu ban ji daga mijina ba. Har yanzu ina cikin jimami. Bana fatan sake komawa Gajiram. Muna cikin hatsari.

Modu Bukar, wadda ya tsere da akuyarsa, yace ya kasa guduwa saboda yana kula da tsoffin iyayensa. Bukar ya bayyana cewa lokacin da ya lura cewa yan ta’addan ba yan farar hula suke kaiwa hari ba, sai ya yanke shawarar kulle kansa da iyayensa da makuli saboda kada su shigo gidan.

"Da muka daina jin harbe-harben sai muka yanke shawarar ci gaba da kasancewa a gidan. A wannan lokacin mun san cewa sojoji ma sun bar wajen saboda sun kwashe tsawon sa’o’i 12 suna fada.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen yan takara da suka yanki fam din takaran gwamnan na APC da PDP a Nasarawa

“Sai gashi a ranar Asabar sun sake dawowa, don haka a wannan lokacin sai nayi tunanin sun dawo kan yan farar hula ne don haka, sai na bar iyayena na gudu. Nayi tafiyar kilomita 7 sai na tsinci kaina a Gajiram inda na shiga mota na koma Maiduguri.”

Ahmed Usman ma wadda ya bayyana irin hakan yace mafi yawancin sojoji basa nan lokacin da harboin ya tsaya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel