Zargin sauya sheka: Ban watsar da yayana ba – Kanin Dankwambo

Zargin sauya sheka: Ban watsar da yayana ba – Kanin Dankwambo

- Buhari Muhammad Dankwambo ya karyata rahoton kafofin watsa labarai na cewa ya yasar da yayansa

- Kanin gwamnan ya kuma kayata cewar ya bar jam'iyyar PDP

- Yace Dankwambon da ake ikirari a kafofin watsa labarai bashi bane

Kanin gwamnan jihar Gombe, Buhari Muhammad Dankwambo ya karyata rahoton kafofin watsa labarai na cewa ya yasar da yayansa, Ibrahim Dankwambo da jam’iyyar PDP.

A wata sanarwa ga manema labarai, kanin Dankwambo ya bayyana rahoton a matsayin mara tushe cewa rade-radi ne kawai.

Ya jadadda cewa yana tare dayayansa cewa shi bai sauya sheka zua jam’iyyar APC kamar yadda ake ta yayatawa.

Zargin sauya sheka: Ban watsar da yayana ba – Kanin Dankwambo
Zargin sauya sheka: Ban watsar da yayana ba – Kanin Dankwambo
Asali: Twitter

Yace gwamnan jihar Gombe uba ne ga dukkanin ahlin gidansu, don haka a zai yi abunda zai bata masa sunansa da martabansa ba.

Ya kara da cewa an kintsa labarin ne don kawai a bata masa suna.

KU KARANTA KUMA: Mune muka haddasa girgizan kasa, mazauna su sa ran ganin wadda yafi na da – Yan asalin Abuja

A bay Legit.ng ta ahoto cewa Buhari Mohammed Dankwambo, jigo a jam'iyyar PDP a jihar Gombe, kuma kanin gwamna Hassan Dankwambo na jihar Gombe ya canja ra'ayinsa kan batun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC kamar yadda ya fadi a ranar Laraba 5 ga watan Satumban 2018.

An tattaro cewa Buhari Dankwambo ya yanke shawarar cigaba da kasancewa a jam'iyyar PDP ne bayan ya yi shawara da 'yan uwansa da kuma sauran aminansa na siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel