Yanzu Yanzu: Boko Haram sun sake kai sabon hari sansanin sojoji a Borno

Yanzu Yanzu: Boko Haram sun sake kai sabon hari sansanin sojoji a Borno

- Boko Haram sun sake kai sabon hari a sansanin sojoji dake Baga, jihar Borno

- Harin ya afku ne kasa da sa'o'i 24 bayan sun kai mamaye yankin Gudumbali dake karamar hukumar Guzamala a jihar

Yan ta’addan Boko Haram sun sake kai sabon hari a sansanin sojoji dake Baga a karamar hukumar Kukawa dake jihar Borno, kwana daya bayan sun mamaye yankin Gudumbali dake karamar hukumar Guzamala sannan suka kori mazauna yankin, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Rundunar sojin Najeriya a ranar Lahadi, 9 ga watan Satumba ta tabbatar da wani harin ta’addanci a Gudumbali, cewa dakarunta na sashi 82 da na bataliya 158 sun dakile harin sannan suka dawo da zaman lafiya a yankin.

Daraktan labarai na rundunar sojin, Birgediya Janar Texas Chukwu yace yan ta’addan sun cinna ma wasu gine-gine wuta a garin amma babu wadda a rasa ransa.

Yanzu Yanzu: Boko Haram sun sake kai sabon hari sansanin sojoji a Borno
Yanzu Yanzu: Boko Haram sun sake kai sabon hari sansanin sojoji a Borno
Asali: Facebook

Majiyarmu ta rahoto cewa a ranar Asabar yan ta’addan Boko Haram sun shigi dakarun soji a Gudumbali sannan suka yasar da mazauna yankin zuwa garin Gubio.

KU KARANTA KUMA: Ba na gudun ayi amfani da na’u’rorin zamani a zaben 2019 – Shugaban kasa Buhari

Idanun saida sun bayyana cewa yan ta’addan sun kama garin bayan sun shiga yankin cikin adadi masu yawa sannan suka fara harbe-harbe wadda hakan yasa subban mazauna yankin tserewa.

An tattaro cewa bayan harin da suka kai Gudumbali, yan ta’addan sun koma Baga a karamar hukumar Kukawa inda suka sake kai wani harin a sansanin sojoji, inda ba’a san adadin mutanen da suka mutu a wuraren biyu ba adaidai lokacin wannan rahoton.

Vanguard ta rahoto cewa Ahmed Salkida, dan jaridar dake da kusanci da yan ta’adda ya bayyana a shafin twitter cewa yan ta’addan na da wani boyayyen kudirin tunda suke ta kai hare-hare sansanin sojoji akai–akai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel