Wasan taka leda: Yan Nigeria sun yarda da Dodo, mu mun yarda da Allah - Kocin Libiya

Wasan taka leda: Yan Nigeria sun yarda da Dodo, mu mun yarda da Allah - Kocin Libiya

- Kocin Libya, Adel Amrouche ya zargi yan Nigeria da yin amfani da dodo a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON)

- A zantawarsa da manema labarai, Amrouche ya jinjinawa yan wasan Afrika ta Kudu, tare da cewar sun fi yan wasan Super Eagles

- Bayan kammala wasan nasu da Afrika ta Kudu, Adel ya ce yana a shirye da karawa da Nigeria saboda su sun yarda da Allah

Kocin da ke horas da yan wasan kasar Libya, Adel Amrouche ya zargi yan Nigeria da yin amfani da dodo a shirin sharar fagen fara gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON), da za'ayi tsakanin kasar ta Libya da Nigeria.

Amrouche ya bayyana hakan bayan da kungiyar kwallon kasar suka buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta Bafana Bafana da ke Afrika ta Kudu, a rukunin wasa na biyu, na wasannin share fagen shiga AFCON.

Wasan da aka tashi canjaras, na nuni da cewa Libya ce ke sama a rukunin nan E da maki 4 kamar dai matsayin Afrika ta Kudu, banbancin kwallaye ne ya sa Libya ta ke a sama, yayin da kungiyar kwallon kafa ta Nigeria (Super Eagles) ke a bayansu da maki 3.

Wasan taka leda: Yan Nigeria sun yarda da Dodo, mu mun yarda da Allah - Kocin Libiya
Wasan taka leda: Yan Nigeria sun yarda da Dodo, mu mun yarda da Allah - Kocin Libiya
Asali: Twitter

KARANTA WANNAN: Ya gamu da ajalisa yana kokowa da kwarton da ya kama turmi da tabarya da matarsa a kan gadon aurensu

A zantawarsa da manema labarai bayan kammala wasan, Amrouche ya jinjinawa abokan karawarsa na Afrika ta Kudu, tare da cewar sun fi yan wasan Super Eagles.

A cikin wani bidiyo da ya mamaye kafafen sada zumunta musamman a shafin Twitter, Amrouche ya bayyana cewa yan wasan Bafana Bafana, sun zarce yan wasan Nigeria wajen buga kwallo, kuma Libya ba zata ji tsoron karawarsu ba.

KARANTA WANNAN: Tura ta kai bango: APC jam'iyyar batattu ce - Makarfi

Ya ce: "Ku yarda da ni, na fi son in buga wasa da Nigeria da in buga da Bafana Bafana, saboda Afrika ta Kudu sun fi yan wasan Super Eagles, ina matukar son ganin na kara da yan wasan Nigeria."

Bayan kammala wasan nasu a filin wasa na Moses Mahbida, Adel ya ce: "Ina a shirye da in kara da Nigeria, su sun yarda da Dodo sosai, mu kuma mun yarda da Allah."

A sabon rahoto:

Kocin da ke horas da yan wasan kasar Libya, Adel Amrouche, ya koma shafinsa na Twitter, inda ya roki gafarar yan wasan kwallon kafa na Nigeria, bisa amfani da kalmar Dodo da yayi a hirarsa da manema labarai.

Adel Amrouche, ya ce yayi amfani da kalmar ne cikin raha, amma yana baiwa daukacin yan wasan Super Eagle hakuri, bisa jingina su da masu amfani da Dodo.

Ya ce yana matukar ganin darajar yan wasan Nigeria, da kuma yadda kasar ta ke martaba wasan taka leda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel