Ghana ta rufe shaguna sama da 40 mallakin yan Nigeria, tare da cafke mutane 100

Ghana ta rufe shaguna sama da 40 mallakin yan Nigeria, tare da cafke mutane 100

- Gwamnatin kasar Ghana, ta rufe sama da shaguna 350 mallakin yan Nigeria, tare da cafke sama da yan Nigeria 100 da ke kasuwanci a kasar

- A watan Augusta, Ghana ta bayyana cewa tana rufe shagunan wadanda suka gaza cimma ka'idoji da dokokin kasar

- Sai dai, wani dan Nigeria da ke kasuwanci a Kumasi, ya ce binciken ya koma kan shagunan yan Nigeria kadai, tare da rokon gwamnatin Nigeria ta sa baki

A Kumasi babban birnin yankin Ashanti a kasar Ghana, sama da shaguna 350 mallakin yan Nigeria ne aka rufe, tare da cafke sama da yan Nigeria 100 da ke kasuwanci a kasar, wadanda a halin yanzu suke garkame a hannun hukumar tsaro da gwamnatin Ghana ta kafa don yiwa fannin saye da sayarwa garambawul a kasar.

Wani dan Nigeria da ke kasuwanci a kasar, ya shaidawa mujallar CFR a wayar tarho cewa, wannan kame da rufe shaguna da gwamnati ta fara yi tun a watan baya, ya gurgunta yan Nigeria da ke yin kasuwanci a kasar.

A lokacin da gwamnatin kasar Ghana ta fara rufe shaguna da kulle mutane a watan Augusta, sun sanar da cewa duk dan kasuwar da aka rufe shagonsa, ya gaza cimma ka'idojin da dokar kasar ta tanar na yin kasuwanci a kasar, wadanda aka kulle kuwa, basu da takardar izinin zama kasar da yin kasuwanci a kasar.

KARANTA WANNAN: Tura ta kai bango: APC jam'iyyar batattu ce - Makarfi

Takun saka: Ghana ta rufe shaguna sama da 370 mallakin yan Nigeria, tare da cafke yan kasuwa 100
Takun saka: Ghana ta rufe shaguna sama da 370 mallakin yan Nigeria, tare da cafke yan kasuwa 100
Asali: Depositphotos

Sai dai, wani dan Nigeria da ke kasuwanci a yankin Kumasi, wanda ya aikawa mujallar CFR hotuna masu motsi da sandararru a ranar Alhamis, ya ce gwamnati ta kirkiro da shirin ne don yin bincike a shagunan yan wata kasa suka mallaka don duba yiyuwar ko suna biyan kudaden haraji ko akasin haka, sai dai yanzu binciken ya koma kan shagunan yan Nigeria kadai.

"A yanzu wannan binciken nasu ya koma kan yan Nigeria. Muna a cikin kungiyar ECOWAS, to don me kuma suke mana haka? Basu shiga shagunan yan kasar Senegal, ko Togo da ke yin kasuwanci tare da mu, shagunan yan Nigeria kawai suke shiga.

Takun saka: Ghana ta rufe shaguna sama da 370 mallakin yan Nigeria, tare da cafke yan kasuwa 100
Takun saka: Ghana ta rufe shaguna sama da 370 mallakin yan Nigeria, tare da cafke yan kasuwa 100
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Ya gamu da ajalisa yana kokowa da kwarton da ya kama turmi da tabarya da matarsa a kan gadon aurensu

"Sun ce wai muna kwace masu ayyuka da kasuwancin su. Ya zama wajibi gwamnatin Nigeria ta tashi tayi wani abu tare da kwato wadanda ake garkame da su. Tun a jiya, sun garkame sama da yan Nigeria 100" a cewar sa.

Hadakar hukumomin da gwamnatin kasar ta kafa don gudanar da wannan aiki, sun hada da jami'an tsaro na kasa, jami'an shige da fice, ma'aikatar harkokin cikin gida, hukumar tabbatar da gudanarwar ayyuka ta Ghana (GSA), ma'aikatar kasuwanci da masana'antu, rundunar yan sanda ta Ghana da kuma kungiyar yan kasuwa ta Ghana (GUTA).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel