Sojojin saman Najeriya sun yi fata-fata da ma'ajiyar makaman 'yan Boko Haram a Sambisa
- Sojin saman Najeriya sun lalata ma'ajiyar makaman 'yan Boko Haram a Sambisa
- Sun ce sun samu nasara a kan 'yan ta'addan
- Sunce wani shwagin sirri sukayi har suka gano su
Jami'an sojojin saman Najeriya dake a cikin rundunar hadin gwuiwa ta Lafiya Dole dake yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan sun sanar da samun gagarumar nasara a kan 'yan ta'addan a maboyar su dake a dajin Sambisa.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: Sabuwar cakwakiya ta bulla a APCn jihar Sokoto
Kamar yadda muka smu, rundunar ta bayyana cewa ta samu yin galaba akan 'yan ta'addan ne tare kuma da yin fata-fata da ma'ajiyar makaman a dajin na Sambisa dake zaman mafaka gare su.
Legit.ng ta samu cewa jami'in hulda da jama'a na jami'an kuma mai magana da yawun su, Air Commodore Ibikunle Daramola shine ya sanarwa da manema labarai hakan a hedikwatar rundunar sojin saman dake a garin Abuja, babban birnin tarayya, Abuja.
Air Commodore Ibikunle Daramola ya kara da cewa wani bincike sirri ne da jami'an su suka gudanar a sararin samaniya suka gano maboyar makaman na 'yan Boko Haram kafin daga bisani su shirya su kuma kai masu hari.
A wani labarin kuma, 'Yan majalisar tarayyar Najeriya mun samu labarin cewa sun dage ranar dawowar su hutun da suka tafi daga 25 ga watan Satumba da muke ciki har zuwa cikin sati na biyu a cikin watan Oktoba mai kamawa.
Wasu 'yan majalisar daga bangaren zauren dattawa da kuma wakilai da wakilin majiyar mu ya zanta da su sun bayyana cewa ranar dawowar ta su ta farko da suka sa kawo yanzu ta tabbata ba zata yiwuba .
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng