Wani dan jarida ya fallasa halin da Sambo Dasuki yake ciki a kurkukun hukumar DSS

Wani dan jarida ya fallasa halin da Sambo Dasuki yake ciki a kurkukun hukumar DSS

- An samu labarin halin da Sambo Dasuki yake ciki a kurkukun hukumar DSS

- An ce inda yake ko makewayi ma babu

- Tun shekarar 2015 ne dai ake tsare da Sambo Dasuki

A cikin wata tattaunawa ta musamman da majiyar mu ta kamfanin jaridar Premium Times ta yi da wannan dan jaridar da jami'an hukumar 'yan sandan sirri na DSS suka tsare kusan kimanin tsawon shekaru biyu ya fadi halin da Sambo Dasuki yake ciki.

Wani dan jarida ya fallasa halin da Sambo Dasuki yake ciki a kurkukun hukumar DSS
Wani dan jarida ya fallasa halin da Sambo Dasuki yake ciki a kurkukun hukumar DSS
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Shekarau ya danganta komawar sa APC da hijirar Manzon Allah

Dan jaridar mai suna Jones Abiri bayan ya fito a 'yan kwanakin nan ya bayyana irin zaman kuncin rayuwa da ya yi tare da sauran wadanda jami'an hukumar ta ke tsare da su suke yi a can ciki kuwa hadda tsohon mai bada shawara a kan harkokin tsaro, na lokacin Goodluck Jonathan, Sambo Dasuki.

Legit.ng ta samu cewa Jones Abiri ya tattabar wa da majiyar tamu cewa ya hadu da Sambo Dasuki duk kuwa da cewa ba a wuri daya aka tsare su ba domin 'su manya' ne.

Sai dai fitaccen dan jaridar ya bayyana cewa a inda Sambo Dasukin yake ko makewayi babu don kuwa a duk lokacin da ya bukaci yin tsugunni, sai dai su fito da shi su kai shi wani wuri can daban.

Ya cigaba da cewa a ta wannan dalilin ne ma suke kan ganshi idan za su raka shi din don a irin wannan lokutan ne ma su ka hadu gaba da gaba, har ma ya mika masa hannu suka gaisa.

A wani labarin kuma, Jami'an sojojin saman Najeriya dake a cikin rundunar hadin gwuiwa ta Lafiya Dole dake yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan sun sanar da samun gagarumar nasara a kan 'yan ta'addan a maboyar su dake a dajin Sambisa.

Kamar yadda muka smu, rundunar ta bayyana cewa ta samu yin galaba akan 'yan ta'addan ne tare kuma da yin fata-fata da ma'ajiyar makaman a dajin na Sambisa dake zaman mafaka gare su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel