Fadar shugaban kasa ta yi karin haske game da zargin cin hancin da akayi wa Abba Kyari

Fadar shugaban kasa ta yi karin haske game da zargin cin hancin da akayi wa Abba Kyari

- Fadar shugaban kasa ta yi karin haske game da zargin cin hancin da akayi wa Abba Kyari

- Tace labarin kanzon kurege ne

- Tace abun takaici ne yadda kafafen yada labarai ke karya

A wani dogon rubutu daga fadar Shugaban kasa dauke da sa hannun mataimakin shugaban kasar na musamman a harkar yada labarai, Malam Garba Shehu, sun karyata da kakkausar murya labarin da aka ce wai Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya karbi cin hanci daga wasu 'yan kwangila.

Fadar shugaban kasa ta yi karin haske game da zargin cin hancin da akayi wa Abba Kyari
Fadar shugaban kasa ta yi karin haske game da zargin cin hancin da akayi wa Abba Kyari
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Yan takara 47 sun yi wa APC tawaye a jihar Katsina

Labarin dai wanda jaridar Punch ta buga ta ce Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya karbi zunzurutun kudin da suka kai Naira miliyan 29 daga wasu 'yan kwangila da nufin ya taimaka masu wajen samun kwangilar siyo ma fadar shugaban kasar motoci.

Legit.ng ta samu cewa sai dai fadar shugaban kasar ta nuna takaicin ta akan labarin da jaridar ta buga sannan ta kuma bukaci 'yan kasar da su yi fatali da labarin domin a cewar su babu kamshin gaskiya a cikin sa ko kadan.

Haka zalika a wani labarin kuma, Masana a fannin ilimin kimiyya da fasaha sun bayyana cewa 'yar girgizar kasar da aka samu a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya a yau din nan na iya kasantuwa ta dalilin fasa duwatsu barkatai da al'umma ke yi.

A don haka ne ma masanan sukayi kira ga mahukunta da su waiwayi batun su kuma yi kokarin samar da dokar da zata hana ayyukan fashe-fashen duwatsun ba bisa ka'ida ba domin kaucewa sake aukuwar lamarin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel